Adsent

Monday, 9 October 2017

GWAMNA BADARU ABUBAKAR YA GANA DA SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YAU A ABUJA...





The Governor of Jigawa State Alhaji Muhammad Badaru Abubakar has today meet with President Muhammadu Buhari at his office in the Aso Rock Presidential Villa, Abuja.

The meeting was to brief the President on the achievements recorded by the two Presidential Committees he (Governor Badaru) is chairing as on Fertilizer and Gas and also the Non Oil Revenue. 

Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a yau ya gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Ofishinsa dake Fadar Shugaban Kasa na Aso Rock, Abuja.

An yi ganawar ne domin shi Maigirma Gwamnan yayi wa Maigirma Shugaban Kasar bayanin irin nasarori da cigabanda Kwamituttuka biyu da shi Maigirma Gwamnan ya samu na Samar da Takin Zamani da Iskar Gas da kuma Kwamitin Samar da Kudaden Shiga a hanyoyin da ba na man fetur ba.

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media.

(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
09/10/2017

Thursday, 5 October 2017

GOVERNOR BADARU SWEARS IN NEW PERMANENT SECRETARIES.



Daga Rabilu S Kadeta Da Ibrahim Matafari Kkm. 


The Jigawa State Governor, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar has today sworn-in the newly appointed Permanent Secretaries in Dutse, the state capital.

Speaking shortly after the swearing in, Governor Muhammad Badaru Abubakar said their appointment and subsequent swearing in  to serve the state government in this capacity is purely on merit, competency and personal integrity while he ‎charged them to be fair and just in the discharge of their duties 

The permanent secretaries sworn in are  Sabo Abdu Babura, Sarki Baba Jahun, Lawan Musa Nadada, Ali Garba Dandidi and Murtala Muhammad Kwalam.

The new Permanent Secretaries were administered the Oath of Office and that of allegiance by the Attorney General and Commissioner of Justice Jigawa State Barr. Sani Hussaini Garun Gabas (SAN) 
**************************************************************************
GWAMNA BADARU YA RANTSAR DA SABBIN SAKATARORI NA DINDINDIN 

Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a yau ya rantsar da Sabbin Sakatarori na Dindindin da aka naɗa kwanan nan. 

A yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan rantsuwar, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar yace naɗin su da rantsuwar kama aiki dda aka yi musu anyi ne bisa la'akari da cancantar su, ƙwarewa da ƙwazon su, don haka yayi kira gare su da su zamo masu adalci da tsantseni wajen gudanar da ayyukan su 

Sabbin Sakatarorin na Dindindin ɗin da aka rantsar sune Sabo Abdu Babura, Sarki Baba Jahun da Lawan Musa Nadada, Ali Garba Dandidi da Murtala Muhammad Kwalam.

Sabbin Sakatarorin na dindindin sun karɓi rantsuwar tasu ne daga babban mai Shari'a kuma Kwamishinan Ma'aikatar Shari'a na Jiha Barista Sani Hussaini Garun  Gabas (SAN). 

Auwal D. Sankara (Fica), 
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media 
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa) 
05/10/2017

Wednesday, 4 October 2017

SHUGABA BUHARI YA NADA GWAMNA BADARU YA JAGORANCI YADDA ZA'A TARA DALA BILYAN TALATIN BA TARE DA HARAJIN MAN FETUR BA...

To improve Nigeria’s non-Oil exports, President Buhari appoint Governor Badaru to head Committee as Nigeria targets $30 Billion non-Oil Revenue 

In order to restructure Nigerian economy, the Federal Government is targeting at least $30 billion revenue from non-oil sources; this will be an increase of $25billion from the current $5 billion.

Nigerian Export Promotion Council (NEPC) Director General Segun Awolowo announced the plan after the National Economic Council (NEC) meeting chaired by Vice – President Yemi Osinbajo at the Presidential Villa.

In order to actualize this dream, the Presidency has constituted a committee to come up with a concise action plan on how to drive non-oil exports based on the presentations and discussions at the Economic Council's meeting. 

Awolowo said the objectives of zero oil plan is to add $150 billion to Nigeria foreign reserves in the next 10 years, create 500,000 jobs, lift 10 million Nigerians out of poverty and integrate each state of the federation into the export value chain.

The focus of the plan is on the export of the following crops: rice, wheat, corn, palm oil, rubber, hides and skin, sugar, soya beans and automotive parts among others, and the destination countries for Nigeria’s exports to include Netherlands, China, Iran, Germany, United Kingdom, France, Spain, Italy, India, Saudi Arabia, among others.

Other members of the committee are the Lagos State Governor Akinwunmi Ambode, Ebonyi State Governor Dave Umahi, Ministers of Industry, Trade & Investment, Agriculture & Rural Development, Power, Works & Housing, Transportation and Finance.

Other members are the (NEPC), NEPZA, NEXIM Bank, and the Central Bank of Nigeria (CBN).

The Committee is expected to submit an initial report by November.
**********************************************************************
Domin inganta Kuɗin Shiga daga ɓangarorin da ba na albarkatun mai ba, Shugaba Buhari ya naɗa Gwamna Badaru ya jagoranci Kwamiti da zai samo hanyar da za a tara Dala Biliyan Talatin daga ɓangarorin da ba na Mai ba

Domin sake fasalin tattalin arzikin Najeriya, gwamnatin tarayya ta ƙudurci aniyar samar da aƙalla Dala Biliyan 30 daga ɓangarorin da ba na albarkatun mai ba, wanda hakan zai samar da ƙarin Dala Biliyan 25 daga Dala Biliyan 5 da ake samu a halin yanzu. 

Darekta Janar na Hukumar Bunƙasa Kayayyakin da ake fitar da su Ƙasashen Waje Segun Awolowo ne ya sanar da haka bayan kammala taron Majalisar Tattalin Arziki na Ƙasa wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar Shugaban Ƙasa. 

Domin cimma wannan burin, fadar ta Shugaban Ƙasa ta kafa wani Kwamiti da zai zaƙulo hanyoyin da za a samar da waɗannan kuɗaɗen shiga daga ɓangarorin da ba na albarkatun mai ba, bayan tattaunawa da muhawarori da aka yi yayin taron Majalisar Tattalin Arziki na Ƙasa. 

Awolowo yace an kafa wannan Kwamiti ne a shirin da gwamnati ke yi na daina dogaro da kuɗaɗen shiga da take samu daga albarkatun man fetur da samar wa Najeriya ƙarin kuɗin asusun ƙasa da ƙasa na Dala Biliyan 150 nan da shekaru goma, samar da ayyukan yi ga mutum 500,000, fitar da ƴan Najeriya sama da Miliyan 10 daga ƙangin talauci da kuma baiwa duk wata Jiha damar fitar da kayayyakin da take sarrafawa zuwa Ƙasashen ƙetare. 

Abinda wannan shiri ya sanya gaba shine fitar da kayayyakin masarufi da albarkatun gona da suka haɗa da shinkafa, alkama, masara, Kwakwa, roba, fatu da ƙiraga, sukari, waken soya da kayayyakin motoci da sauran su zuwa Ƙasashen da Najeriya take hulɗar kasuwanci da su irin Holland, Sin, Iran, Jamus, Ingila, Faransa, Andalus, Italiya, India, Saudi Arabia da sauran su. 

Sauran Mambobin Kwamitin sun haɗa da gwamnonin Lagos da Ebonyi wato Akinwunmi Ambode, da Dave Umuahia, Ministocin Masana'antu, Cinikayya da Zuba Jari, Albarkatun Noma da Raya Karkara, Wuta, Ayyuka da Gidaje, Sufuri da Kuɗi. 

Sauran sun haɗa da hukumomin NEPC, NEPZA, Bankin NEXIM, Babban Bankin Najeriya (CBN).

Ana sa ran Kwamitin zata miƙa rahoton ta na farko a watan Nuwamba mai zuwa. 

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
04/10/2017

Tuesday, 3 October 2017

GWAMNA BADARU ABUBAKAR YA ZIYARCI GIDAN MARIGAYI AVM MUKHTAR A YAU.



The Governor of Jigawa State Alhaji Muhammad Badaru Abubakar was this morning among the early callers to pay a condolence visit on the family of Late Wazirin Dutse, Air Vice Marshal Moukhtar Muhammad, former military governor of Kaduna State during the military era. 

Governor Badaru said the late elder statesman epitomizes sincerity and said his wise counsel will be greatly missed.

Late AVM Moukhtar Muhammed, died at London Hospital. His body will arrive Nigeria this evening from England where thousands of sympathizers including the Governor will receive him to pay him their last respect.

The Governor described the late AVM Moukhtar as a man who will be remembered for his sterling qualities of up rightness and selflessness.

The governor condoled with the family of the Chairman of the Board of Directors of Freedom Radio who is also the vice Chairman of Arewa Consultative Forum (ACF), and urged them to take solace in his good deeds and the legacies he left behind.
**********************************************
Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar da sanyin safiyar nan ya ziyarci gidan Iyalan Marigayi Wazirin Dutse Wazirin Dutse, AVM Moukhtar Muhammad, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a lokacin mulkin soji. 

Gwamna Badaru yace a lokacin rayuwar Marigayin wanda ɗaya ne daga cikin Dattawan ƙasar nan, ya nuna dattaku da gaskiya, kuma za a rasa irin shawarwari masu amfani da ya saba bayarwa. 

Marigayi AVM Moukhtar Muhammed, ya rasu ne a wani asibiti dake Birnin Landan. Ana kuma sa ran gawar sa zai iso Najeriya daga ƙasar Ingila inda dubban jama'a ciki har da Maigirma Gwamnan zasu karɓi gawar don yi masa Sallah. 

Gwamna Badaru yace za a cigaba da tuna Marigayi Wazirin Dutse da kyawawan halayen sa da kamalar sa da kuma son cigaban al'uma. 

Gwamnan ya kuma miƙa ta'aziyyar sa ga Iyalan Marigayi Mukhtar Muhammad, wanda kuma kafin rasuwar sa shine Shugaban Darektoci na Gidan Rediyo  Freedom kuma Mataimakin Shugaban Dattawan Arewa (ACF) inda yace su ɗauki dangana da tunawa da irin abubuwan alheri da ya shuka a yayin da yake raye. 

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
03/10/2017

Monday, 2 October 2017

GWAMNA BADARU ABUBAKAR YA BAYYANA RASUWAR AVM MUKHTAR A MATSAYIN BUBBAN RASHI.


Daga Mustee Badala.
Tsinkaya
                Social
                           Network

Gwamna Badaru yayi Jimamin Rasuwar Marigayi Wazirin Dutse; yace Jigawa tayi Rashin Babban Ɗa! Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana rasuwar AVM Mukhtar Muhammad's death a matsayin babban rashi ga jihar Jigawa dama Najeriya baki ɗaya.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya samu labarin rasuwar AVM Mukhtar Muhammad a sanyin safiyar Litinin. Gwamna Badaru yace duk da cewa duk mai rai dole ne ya ɗanɗani mutuwa, amma rashin mutum irin AVM Mukhtar Muhammad babban rashi ne.

AVM Mukhtar Muhammad wanda yake riƙe da Sarautar Wazirin Dutse, tsohon Gwamnan Soji ne na Jihar Kaduna, kuma Shugaban Darektocin Tashar Rediyo mai zaman kanta na farko a Arewa wato Freedom Radio Kano, ya rasu ne a wani asibiti dake birnin Landan bayan yasha fama da rashin lafiya.

Gwamna Badaru yace za a cigaba da tuna Marigayi Wazirin Dutse da kyawawan halayen sa da kamalar sa da kuma son cigaban al'uma. Gwamnan ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya musamman al'umar Jihar Jigawa da su yi koyi da irin halayen sa da ƙoƙarin da yake yi na haɗa kan al'umar ƙasar nan. Gwamnan ya kuma miƙa ta'aziyyar sa ga Iyalan Marigayi Mukhtar Muhammad, inda yace su ɗauki dangana da tunawa da irin abubuwan alheri da ya shuka a yayin da yake raye.

A ƙarshe Gwamna Badaru yace gwamnatin sa zata yi rashin mai bata shawara nagari.

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media (Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)

Mustee Badala
New media Correspondent
02/10/2017

Sunday, 1 October 2017

DAGA MA'AIKATAR LAFIYA TA JIHAR JIGAWA.


JIGAWA STATE MINISTRY OF HEALTH

Gwamnatin jihar jigawa karkashin jagorancin gwamna Badaru Abubakar,  ta fitar da sabon jadawalin bada abinci a manyan  asibitocin jihar nan ga marassa lafiya.
Kwamishinan lafiya Dr.Abba Zakari ya bada umarnin sake fasalin sabon jadawalin domin dacewa da yanayin samun saukin marassa lafiya.

Kwamishinan ya Kara da Cewa jadawalin ya fara aiki daga Yau 01 October 2017 kuma ana sanar da al'umma duk Wanda ya tarar sabanin abin da yake jadawalin ka kira 07038379934, 07065934753.

Gwamnatin ta jihar Jigawa tana bada fifiko ga bangaren lafiya, sakamakon Lafiya itace gaba da komai, Kwamishinan Lafiya Dr. Abba ya kware wajen Inganta harkar lafiya domin daga zamansa Kwamishina ma'aikatar lafiya ta samu kyawawan tsare tsare don inganta lafiya. 

Rahoto daga Rabilu S Kadeta
Chairman Tsinkaya Social Network Gagarawa Chapter

Saturday, 30 September 2017

AN BAYYANA MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR JIGAWA BARR. IBRAHIM HASSAN HADEJIA A MATSAYIN MUTUM MAI GASKIYA DA RIKON AMANA.


Tsohon shugaban hukumar ilimin bai daya a matakin farko na jihar Jigawa Hon. Dabuwa Kiri Kasamma ya bayyana haka a wajen bikin kaddamar da shugabancin kungiyar Barr. Ibrahim Hassan media global reshen karamar hukumar Kiri Kasamma karkashin jagorancin Yusuf Tama Mai Aski.
Yace shine wadda ya rike mukamai daban-daban a gwamnati amma har yanzu ba'a taba samunsa da handama da babakere da dukiyar al'umma ba.

An zabi Usman Sa'idu Madachi a matsayin shugaba Abba Muhammad Malami sakatare sai Dahiru Aminu Madachi Ma'aji Ya'u Abdullahi Walwala sai Yani Kiri Kasamma shugabar mata.

Tun a farko Shugaban karamar hukumar Kiri Kasamma Hon. Salisu Kubayau ya nuna gamsuwarsa da wannan kungiya, tare da bada dukkan gudunmawa wadda ba tafi karfinsa ba akan gudanarwar kungiyar kamar yadda yayi alkawari.

A nasa jawabin shugaban kungiyar reshen karamar hukumar Kiri Kasamma ya nanu farin cikinsa bisa amincewar "ya"yan kungiyar, tare da neman hadin kansu domin a gudu tare a tsira tare. Taron ya samu halartar tsohon kwamishinan watsa labarai matasa da wasanni Hon. Mukhtar Birniwa .
Allah ya taimaki gwamnatin Sardauna/Shettima Allah kayi musu jagora.

YAKUBU GARBA HADEJIA ALGON CHAIRMAN JIGAWA STATE APC SOCIAL MEDIA HADEJIA SENATORIAL ZONE.

GWAMNA BADARU NA JIHAR JIGAWA YA INGANTA RUWAN SHA..


Daga Rabilu S. Kadeta
GWAMNATIN JIHAR JIGAWA TANA CIGABA DA INGANTA HANYOYIN SAMAR DA RUWANSHA A BIRNI DA KAUYUKA. 

Hukumar samarda ruwansha da kuma tsaftar mahalli ta jihar jigawa RUWASA ta tona fanfunan Tuka tuka Dubu Daya da Dari Shida da Ashirin da Biyu (1,122) a sassan jihar nan.

Manajan Daraktan hukumar Injiniya Labaran Adamu ya sanar da hakan.

Yace Gwamnati ta kashe kudi naira miliyan 445 wajen tona fanfunan a tsakanin Shekara ta 2015 zuwa yanzu.

Injiniya Labaran Adamu ya kara da cewar hukumar ta gyara fanfunan tuka tuka Dubu Hudu da Dari Daya da Casa'in da Biyar (4,195) akan kudi naira miliyan case'in da biyu 92.

Rabilu S Kadeta
Chairman
Tsinkaya Social Network Gagarawa Chapter

GWAMNA BADARU YANA KAI ZIYARA CIBIYOYIN LAFIYA...



In continuation of his inspections to health Facilities and other projects within the state, the Governor of Jigawa State Alhaji Muhammad Badaru Abubakar has today inspected the Kazaure General Hospital, Psychiatric Hospital and also the land allocated for the construction Specialist Hospital. 

Governor Badaru called on the contractors handling the project of the construction of the specialist hospital to speed up work in order to meet up with the time alloted for the project, while at the psychiatric hospital, Governor Badaru promised that his administration will equip the psychiatric hospital in order to better the living standard and welfare of the inmates. 

Governor Badaru also inspected the on-going Kazaure Township Roads and drainages being constructed in the Emir's Palace Road. 

Governor Badaru also visited Primary Healthcare Centers in Roni, Gwiwa, Yankwashi before proceeding to Government Science Secondary School Kanya Babba in Babura Local Government. 

At the GSSS Kanya Babba, after listening to the pleas of the school management on lack of portable water, promised to come to their aid as soon as earnest. 
****************************************
A cigaba da ziyarar da yake kaiwa cibiyoyin lafiya da wasu muhimman ayyuka a faɗin Jiha, Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a yau ya kai ziyarar gani da ido a Babban Asibitin garin Kazaure, Asibitin Mahaukata na Kazaure da duba filin da aka ware domin gina Asibitin Ƙwararru na Kazaure. 

Maigirma Gwamnan yayi kira ga ƴan kwangilar dake aikin Asibitin Ƙwararrun da su hanzarta kammala aikin a lokacin da aka ƙayyade musu, a inda kuma a ziyarar da ya kai asibitin Mahaukata yayi alƙawarin cewa gwamnatin sa zata gyara asibitin domin inganta kula da lafiyar majinyatan. 

Duk a cikin garin Kazaure, Gwamna Badaru ya duba ayyukan titunan cikin gari da ake yi a halin yanzu, tare da duba magudanan ruwa da ake yi a wajen ƙofar Fadar Kazaure. 

Gwamna Badaru ya kuma kai ziyara ɗakunan sha magani na sha ka tafi na garuruwan Roni, Gwiwa, da Yankwashi kafin ya zarce zuwa Makarantar Sakandiren Kimiyya na Kanya Babba dake Ƙaramar Hukumar Babura. 

A Sakandiren Kimiyyar na Kanya Babba, bayan jin ƙorafin hukumar makarantar na rashin ruwa, Maigirma Gwamnan yayi alƙawarin kawo masa ɗauki cikin gaggawa. 

Auwal D. Sankara (Fica), 
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media 
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa) 
25/09/2017

Friday, 29 September 2017

ZA'A DAUKI MALAMAN MAKARANTA 2,000 A JIGAWA.


Daga Rabilu S. Kadeta.... 
Shirin Daukan Malaman Makaranta Yayi Nisa a Jihar Jigawa Karkashin Jagorancin Gwamna Badaru.

Gwamnatin jihar jigawa ta kammala shirye shiryen daukar malamai dubu biyu (2,000) aiki a wani mataki na farfado da bangaren ilmi, Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya sanar da hakan a lokacin babban taron wakilan kungiyar malamai karo na shida da aka gudanar a Kazaure.

HOS All is now set for the recruitment of two thousand teachers by the Jigawa state government as part of effort to revitalize the education sector in the state. Governor Muhammad Badaru Abubakar made this known in a message to the 6th quadrennial state delegates’ conference of the Nigeria Union of Teachers held in Kazaure.

The Governor who was represented by the state Head of Service, Alhaji Muhammad Inuwa Tahir, said government has allocated thirty two percent of this year`s budget to education. He reiterated government`s commitment to revamp education sector.
On his part the outgoing chairman of the Nigeria Union of Teachers, Comrade Usman Ya`u Dutse commended teachers in the state for the support and cooperation given to him during his tenure. Announcing the result the chief returning officer of the election, Dr.Nnnena Okonkwo said Abdulkadir Yunusa emerged chairman, Dauda Sha`aibu deputy chairman, Bashari Abdullahi 1st vice-chairman, while Aliyu Shehu Limawa was elected 2nd vice-chairman.
Others include Alhassan Madaki treasurer, Haruna Abdu Publicly secretary and Yahaya Abdu social secretary. COV/SU/MAG/BS

From Shuaibu kabeer gumel Auditor gener tsinkaya social net gumel chapter 07062857958
And
Rabilu S KadetaChairman Tsinkaya Social Network Gagarawa Chapter. 

Sunday, 18 June 2017

KOTU TA YANKE WA WANI MATASHI HUKUNCIN KISA A JIHAR JIGAWA..... Daga Saifullahi Abbas Hadejia



MA'AIKATAR SHARI'A DAKE JIHAR JIGAWA


Wata Kotu a  Jihar Jigawa Karkashin Jagorancin Kwamishinan Shari'a na jihar Barr. Sani Husssini G/Gabas ta yanke hukuncin kisa ta hanyar Rataya ga wani matashi...  

 Kotun Shari'a Dake Birnin Kudu High Court 2 Ta Yankewa Adamu Audu Dan Shekara 35 Mazaunin Kauyen Tudun Malam Dake Karamar Hukumar Birnin Kudu Jihar Jigawa, Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya!

  A Ranar 1-4-2015 Da Misalin Karfe 12 Na Rana, Wani Mutum Mai Suna Adamu Audu Wanda Ake Tuhumar Sa Da Kisan Kai Ta Hanyar Cakawa Wani Matashi Wuka A Ciki,  Mai Suna Garba Khalid Dan Shekara 30, Mazaunin Kauyen Tudun Malam Dake Karamar Hukumar Birnin Kudu, Cikin Jihar Jigawa.

 Bayan Kotu Ta Tabbatar Da Laifin Kisan Kai A Kansa Wajen Samun Gamsassun Shaidu, Da Kuma Ikrari Da Yayi Da Bakinsa, Alkalin Kotun Hon. Judge. Ahmed Mohammed Kazaure. Wanda A Jawabin Makashin Yace, Yana Zargin Marigayinne Da Maita, Hakan Yasa Ya Kashe Shi. Wanda Kotu Tace Masa Wannan Bazai Zama Hujja A Gareshi Ba

 Kotu Ta Yanke Masa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Karkashin Kashi Na 221 Kundin Laifuffuka Na Jihar Jigawa (Jigawa State Fenal Code Section 221)

    Allah ka tsaremu da biye wa zuciya.

-Saifullahi Abbas Hadejia
 New Media Correspondent
 Ministry Of Justice
 Jigawa State, Nigeria

Wednesday, 31 May 2017

LABARAN JIHAR JIGAWA....




31-05-2017                  RADIO
Gidan redion Jigawa da sauran tashoshin FM zasu gabatar da muku da shiri na musamman kan alamurran siyasar jihar nan cikin shekaru biyu na mulkin gwamna Badaru Abubakar shirin zai zo muku ne da misalin karfe tara na daren yau zuwa tara da minti arbain da biyar sannan a maimata shirin a gobe alhamis da misalin karfe tara da rabi na safe zuwa goma da minti goma sha biyar na safe

31-05-2017                            BIRNIN KUDU
An kaddamar da sabbin shugabannin majalissar matasa ta K. H Birnin Kudu. Wadanda aka kaddamar sun hadar da Comrade Sanusi Idris shugaba da Kabiru Garba Wurno mataimakin shugaba da  Maharazu Umar Maaji da Abdulrazak Muhammad sakataren kudi da Auwal Iiliyasu PRO da kuma Haruna Isa sakataren majalissar.

A jawabinsa wajen bikin kaddamar da shugabannin majalisar  Matasan, mataimakin na musamman ga gwamna kan harkokin matasa Alhaji Salisu Rabiu Babura ya nanata kudirin gwamnati na samarwa matasa hanyoyin dogaro da kai a bangarori daban daban. A jawabinsa shugaban kwamitin riko na yankin Mallam Adamu Garba ya yi alkawarin bada ofishi ga majalissar.

Ya kuma bukaci matasan dasu guji shan miyagun kwayoyi da munanan dabiu. A jawabinsa na godiya shugaban majalissar Comrade Sanusi Idris yace majalissar itace lemar duk wata kungiya ta matasa a kasar nan Daga bisani dan majalissar wakilai ta kasa Injiniya Magaji Dau ALiyu ya baiwa majalisar gudunmawar naira dubu hamsin. 

31-05-2017                 KIYAWA
An yi kira gay an kwangila dake gudanar da aikin gyaran masalatan jumaa na garuruwan Kiyawa da Katanga dasu maida hankali wajen kammala aikin akan lokaci. Shugaban kwamitin riko na yankin Abdullahi Suleiman Yayari ya yi bukatar a lokacin ziyarar gani da ido. Yace KH ta biya sauran kason kudin aikin da ya rage domin baiwa yan kwangilar damar kammala aikin akan lokaci. Alhaji Abdullahi Suleiman ya yi fatan zasu gudanar da aiki mai inganci. 

31-05-2017                              HADEJIA
Mai martaba sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Hadejia  ya bude karatun tafsir na watan Ramadan a gidan kurkuku na Mawadaci. A jawabinsa mai martaba sarki ya bukaci masu abin hannu dasu tallafawa wadanda suke zaune a gidaje yari domin tallafawa rayuwarsu Ya ce mazauan gidajen yari suna bukatar tallafi Sarkin ya kuma duba irin kayayyakin da daurarru suke sarrafawa. 
A jawabinsa wakilin shugaban gidan yari na jiha ASP Adam Muhammad Bello ya yabawa sarkin bisa damuwarsa ga gidan yarin. 

31-05-2017                          TAKUR
An yi kira ga hukumar gidaje ta jihar Jigawa da ta yashe magudanan ruwa da kwalbatoci a unguwar Takur domin gudun ambaliyar ruwa. Mazauna unguwar sun bayyana cewar sakamakon mamakon ruwan saman da aka gudanar a wannan rana , layuka da kuma gidaje da dama sun cika da ruwa makil sakamakon cikewar magudanan ruwan da kwalbatocin unguwannin suka yi. Wani magidanci Mallam Musa ya ce ruwan ya mamaye layinsu ta yadda sai mutum ya tattare wando yake samun hanyar fita.

Daga nan sai ya bukaci hukumar data taimaka wajen yashe magudanan ruwan domin gudun ambaliyar ruwa. Haka zalika suma mazauna unguwar gida dubu yadin dutse sun roki hukumar gidaje ta jiha data kai musu dauki ta yadda wasu layukan ke cika da ruwan sama da zarar an samu mamakon ruwa. wani mazaunin unguwar Mallam Anas yace muddin aka yi ruwa to suna fargaba shiga gidajen su musamman mazauna layin dibinai. 

31-5-2017                         BUJI
Shirin yaki da yunwa na majalisar dinkin duniya a karamar hukumar Buji ya raba kudi naira miliyan talatin da tara ga mata masu juna biyu da kananan yara dubu tara da dari biyu da casa’in da tara.

Jami’in kula da shirin a karamar hukumar,Malam Abdullahi Muhammad ya bayyana haka lokacin taro da kwamatin masu ruwa da tsaki na yankin. Ya ce tuni aka ya yaye mata dari tara da biyar wadanda suka ci gajiyar shirin na tsawon watanni talatin, inda ya bukace su su yi kyakkyawan amfani da kudaden da aka ba su.

A jawabinsa shugaban kwamatin riko na karamar hukumar Alhaji Hashim Ahmad Fagam ya bada tabbacin karamar hukumar na ci gaba tallafawa shirin domin cimma burin da aka sanya a gaba.

31-5-2017                      GWARAM
Karamar hukumar Gwaram ta tallafawa yan asalin yankin wadanda zasu tantancewar shiga aikin soja kimanin saba’in da takwas da kudin mota da kuma na abinci. Shugaban kwamatin riko na karamar hukumar Alhaji Umar Illu Shuwarin ya bayyana haka lokacin da yake jawabin ban kwana ga matasan a sakatariyar karamar hukumar.

Ya bukace su, su kasance masu juriya da zama jakadu na gari wajen karbar horon aikin soja. Shugaban wanda ya sami wakilcin sakataren karamar hukumar Alhaji Yakubu Abdullahi ya ce a shirye suke su tallafawa dukkanin dan asalin yankin da ya sami wata dama ta samun aiki musamma a matakin tarayya.

31-5-2017                        LAFIYA
Gwamnatin jihar Jigawa ta bude tayin bada kwangilar aikin gina sabon asibitin kwararru a garin Hadejia. Da yake jawabi a wajen bude bada tayin kwangilar, kwamishinam lafiya na jiha, Dakta Abba Zakari ya ce gwamnati ta kudiri niyyar gina sabon asibitin kwararrun ne domin maye-gurbin asibitin kwararru na Reshid Shekoni wanda jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutse ta karba domin mayar da shi asibitin koyarwa.

Dakta Abba Zakari ya ce gwamnatin jiha ta damu da ganin ta fadada ayyukan kwararru a fanin kiwon lafiya zuwa kowane loko da sako na jihar nan. Ya ce kamfanoni fiye da ashirin ne suka nuna sha’awarsu ta neman kwangilar, inda daga bisani biyar daga cikinsu suka cancanta , yayin da suka gabatar da takardunsu ga kwamatin tantance kamfanonin.

A jawabinsa babban sakataren ma’aikatar lafiya, Dakta Muhammad Abdullahi ya bukaci kamfanonin da zasu yi nasara su tabbatar sun gudanar da aiki mai inganci. Daya daga cikin wakilan kamfanonin kuma wakilin kamfanin PACHE-NIG LTD, Sakkis Abi ya bada tabbacin yin aiki mai kyau da zarar sun sami nasara.

 31-5-2017                            RUWA
Ma’aikatar albarkatun ruwa ta jihar Jigawa ta bude tayin bada kwangilar haka rijiyoyin tuka-tuka dari da talatin da shida a mazabu yan majalisar dokokin jiha talatin. Da yake jawabi wajen bude tayin bada kwangilar, Kwamishinan ma’aikatar Alhaji Ibrahim Garba Hannun-Gwiwa ya ce an ware fiye da naira miliyan dari da ashirin da uku domin gudanar da aikin.

Kwamishinan wanda ya sami wakilcin manajan daraktan hukumar samar da ruwan sha a matsakaitan garuruwa, Injiniyya Labaran Adamu ya ce kamfanoni hamsin da daya ne suka shiga tayin bada kwangilar, inda ya bukaci kamfanonin da suka sami nasara su yi aiki mai inganci.

A jawabinsa wakilin kamfanonin da suka sami nasara Alhaji Ma’azu Ma’zau ya yi alkawarin yin aiki mai kyau da kuma inganci.

31-5-2017                              YUGUDA
An yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa aniyarta na gina hanyar Gwaram zuwa Basirka a yankin karamar hukumar Gwaram. Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar karamar hukumar, Alhaji Yuguda Hassan Kila ya yi wannan yabo, jim kadan da kaddamar da gadar Sagi dake kan hanyar Gwaram zuwa Basirka.

Wakilinmu Muhammad Sabo Kila nada karin bayani... 

Alhaji Yuguda Hassan Kila wanda ya bayyana gamsuwa kan kudirin gwamna Muhammad Badaru Abubakar na sake gina hanyar Gwaram zuwa Basirka, ya ce hanyar wace ta hade jihohi da dama zata kara habaka tattalin arziki dana sufuri a tsakanin jigawa da sauran jihohi.

Dan majalisar wakilan ya ce kasancewar ya gabatar da kudirin sake gina hanyar a zauren majalisar wakilai ta kasa, ya ce koda gwamnan ya gudanar da aikin sake gina hanyar lashakkah gwamnatin tarayya zata biya shi kudin aikinsa daga baya.

Alhaji Yuguda Hassan Kila ya kara da cewa akwai ayyuka da dama da wannan gwamnati ta bujiro da su domin ingata rayuwar al’umma a kowane mataki, sai dai kuma ya bukaci al’umma su ci gaba da hakuri da kuma marawa gwamnati baya. 

Daga Profile din Hussaini Hadejia. 

Saturday, 20 May 2017

GWAMNA BADARU YA KARƁI BAƘUNCIN SHUGABAR CIBIYAR CINIKAYYA...




Governor Muhammad Badaru Abubakar has stressed the need for partnership with the private sector to industrialize the Northern States.

The governor stated this when he received the Chairperson of the Conference of Northern Nigeria Chamber of Commerce, Industry, Mines and Agriculture, Hajia Saratu Iya Aliyu at the Government House.

He said it is only through collaboration with the private sector that the region will explore its potential thereby creating jobs for the teaming youths.

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar said his administration has done a lot in attracting investors to invest in the state.

Earlier in her speech the chairperson, Hajiya Saratu Iya Aliyu commended Governor Muhammad Bafaru Abubakar for his effort towards transforming Jigawa State.
******************************************
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana bukatar gwamnatoci da su hada kai da yan kasuwa domin samar da masana'antu a Jihohin Arewacin Najeriya. 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da ya karbi bakuncin Shugaban Cibiyar Cinikayya, Masana'antu, Hako Ma'adinai da Harkar Noma da Jihohin Arewacin Najeriya, Hajia Saratu Iya Aliyu a gidan Gwamnatin Jihar Jigawa. 

Yace ta haka ne kaɗai shiyyar zata iya cimma muradun ta na samar wa ɗumbin matasan dake yankin ayyukan yi. 

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar yace gwamnatin sa tayi iyakacin kokarin ta na samo masu zuba jari a Jihar 

Tun farko a nata jawabin Shugaban Cibiyar Hajiya Saratu Iya Aliyu ta yabawa Gwamna Muhammad Badaru a kokarin da yake yi wajen kawo cigaba a Jihar. 

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media 
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa) 
20/05/2017

Monday, 15 May 2017

BAN KWANA DA SABI'U MIKO 'YANDUTSE...

                      TSINKAYA SOCIAL NETWORK...... 


BAN KWANA DA SABI'U MIKO 'YANDUTSE... 

Haƙiƙa dukkanin mai Rai Mamaci ne kamar yadda Allah (swa) ya faɗi a cikin Alƙur' ani mai tsarki,  A yau da misalin ƙarfe goma na safe naga Rubutun Sabi'u Miko yana neman Addu'a domin yana kan hanya zuwa Hadejia. Koda mukayi waya dashi nace masa bana Hadejia da nazo mun gaisa, yace babu damuwa watarana zamu hadu in Allah ya so. Yanzu na samu labarin Rasuwar wannan Bawan Allah dan Gwagwarmaya mai kishin Al'ummar sa, kuma mutum mai fara'a da kamun kai. Hakika Jigawa State Social Media Team munyi rashi sai dai muce Allah ya gafarta masa da rahama ya yafe masa kurakuran sa. 

Sabi'u Miko 'Yandutse mutum ne mai ra'ayi wadda kuma ra'ayinsa bai sanya ya bata da mutane ba, duk rubuce rubucensa a social media bai wuce bayyana ra'ayinsa ba. Allah ya kyauta kwanciya Sabi'u Miko, Allah ya Albarkaci Iyalan da ka bari. 

Sabi'u Miko yana daga cikin waɗanda muka kafa Apc Social media dashi, kuma duk abinda ake na Social media a Jihar Jigawa dashi akeyi, a duk lokacin da yaga anyi Posting wadda bai kamata ba ko a Dandalin Siyasa ko a Apc Social media ko a Tsinkaya, yakan kira na a waya yace in da hali a cire. Kokuma ya min sako ta Inbox a facebook. Allahu Akbar! 

A yau Litinin akan hanyarsa ta komawa gida 'yandutse Hatsarin mota ya rutsa dashi inda ya rasa rayuwarsa. To ba gaggawa yayi ba, muma da muka rage ba jinkiri muka yi ba. Allah yasa mu mutu muna masu imani. 

A madadin ƙungiyar Tsinkaya Social Network ƙarƙashin Jagorancin Habu Badala Gumel, muna meƙa Saƙon Ta'aziyya ga Gwamnatin Jihar Jigawa da Ofishin S. A. New Media Jigawa da Apc Social Media da Crew da sauran Al'ummar Jihar Jigawa, musamman Masarautar Ringim. Muna musu Ta'aziyya Allah ya gafarta masa da rahama ya kyauta makwancin sa Ameen.