Daga Rabilu S. Kadeta
GWAMNATIN JIHAR JIGAWA TANA CIGABA DA INGANTA HANYOYIN SAMAR DA RUWANSHA A BIRNI DA KAUYUKA.
Hukumar samarda ruwansha da kuma tsaftar mahalli ta jihar jigawa RUWASA ta tona fanfunan Tuka tuka Dubu Daya da Dari Shida da Ashirin da Biyu (1,122) a sassan jihar nan.
Manajan Daraktan hukumar Injiniya Labaran Adamu ya sanar da hakan.
Yace Gwamnati ta kashe kudi naira miliyan 445 wajen tona fanfunan a tsakanin Shekara ta 2015 zuwa yanzu.
Injiniya Labaran Adamu ya kara da cewar hukumar ta gyara fanfunan tuka tuka Dubu Hudu da Dari Daya da Casa'in da Biyar (4,195) akan kudi naira miliyan case'in da biyu 92.
Rabilu S Kadeta
Chairman
Tsinkaya Social Network Gagarawa Chapter
No comments:
Post a Comment