Adsent

Saturday, 30 September 2017

AN BAYYANA MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR JIGAWA BARR. IBRAHIM HASSAN HADEJIA A MATSAYIN MUTUM MAI GASKIYA DA RIKON AMANA.


Tsohon shugaban hukumar ilimin bai daya a matakin farko na jihar Jigawa Hon. Dabuwa Kiri Kasamma ya bayyana haka a wajen bikin kaddamar da shugabancin kungiyar Barr. Ibrahim Hassan media global reshen karamar hukumar Kiri Kasamma karkashin jagorancin Yusuf Tama Mai Aski.
Yace shine wadda ya rike mukamai daban-daban a gwamnati amma har yanzu ba'a taba samunsa da handama da babakere da dukiyar al'umma ba.

An zabi Usman Sa'idu Madachi a matsayin shugaba Abba Muhammad Malami sakatare sai Dahiru Aminu Madachi Ma'aji Ya'u Abdullahi Walwala sai Yani Kiri Kasamma shugabar mata.

Tun a farko Shugaban karamar hukumar Kiri Kasamma Hon. Salisu Kubayau ya nuna gamsuwarsa da wannan kungiya, tare da bada dukkan gudunmawa wadda ba tafi karfinsa ba akan gudanarwar kungiyar kamar yadda yayi alkawari.

A nasa jawabin shugaban kungiyar reshen karamar hukumar Kiri Kasamma ya nanu farin cikinsa bisa amincewar "ya"yan kungiyar, tare da neman hadin kansu domin a gudu tare a tsira tare. Taron ya samu halartar tsohon kwamishinan watsa labarai matasa da wasanni Hon. Mukhtar Birniwa .
Allah ya taimaki gwamnatin Sardauna/Shettima Allah kayi musu jagora.

YAKUBU GARBA HADEJIA ALGON CHAIRMAN JIGAWA STATE APC SOCIAL MEDIA HADEJIA SENATORIAL ZONE.

No comments: