JIGAWA STATE MINISTRY OF HEALTH
Gwamnatin jihar jigawa karkashin jagorancin gwamna Badaru Abubakar, ta fitar da sabon jadawalin bada abinci a manyan asibitocin jihar nan ga marassa lafiya.
Kwamishinan lafiya Dr.Abba Zakari ya bada umarnin sake fasalin sabon jadawalin domin dacewa da yanayin samun saukin marassa lafiya.
Kwamishinan ya Kara da Cewa jadawalin ya fara aiki daga Yau 01 October 2017 kuma ana sanar da al'umma duk Wanda ya tarar sabanin abin da yake jadawalin ka kira 07038379934, 07065934753.
Gwamnatin ta jihar Jigawa tana bada fifiko ga bangaren lafiya, sakamakon Lafiya itace gaba da komai, Kwamishinan Lafiya Dr. Abba ya kware wajen Inganta harkar lafiya domin daga zamansa Kwamishina ma'aikatar lafiya ta samu kyawawan tsare tsare don inganta lafiya.
Rahoto daga Rabilu S Kadeta
Chairman Tsinkaya Social Network Gagarawa Chapter
No comments:
Post a Comment