Adsent

Tuesday, 3 October 2017

GWAMNA BADARU ABUBAKAR YA ZIYARCI GIDAN MARIGAYI AVM MUKHTAR A YAU.



The Governor of Jigawa State Alhaji Muhammad Badaru Abubakar was this morning among the early callers to pay a condolence visit on the family of Late Wazirin Dutse, Air Vice Marshal Moukhtar Muhammad, former military governor of Kaduna State during the military era. 

Governor Badaru said the late elder statesman epitomizes sincerity and said his wise counsel will be greatly missed.

Late AVM Moukhtar Muhammed, died at London Hospital. His body will arrive Nigeria this evening from England where thousands of sympathizers including the Governor will receive him to pay him their last respect.

The Governor described the late AVM Moukhtar as a man who will be remembered for his sterling qualities of up rightness and selflessness.

The governor condoled with the family of the Chairman of the Board of Directors of Freedom Radio who is also the vice Chairman of Arewa Consultative Forum (ACF), and urged them to take solace in his good deeds and the legacies he left behind.
**********************************************
Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar da sanyin safiyar nan ya ziyarci gidan Iyalan Marigayi Wazirin Dutse Wazirin Dutse, AVM Moukhtar Muhammad, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a lokacin mulkin soji. 

Gwamna Badaru yace a lokacin rayuwar Marigayin wanda ɗaya ne daga cikin Dattawan ƙasar nan, ya nuna dattaku da gaskiya, kuma za a rasa irin shawarwari masu amfani da ya saba bayarwa. 

Marigayi AVM Moukhtar Muhammed, ya rasu ne a wani asibiti dake Birnin Landan. Ana kuma sa ran gawar sa zai iso Najeriya daga ƙasar Ingila inda dubban jama'a ciki har da Maigirma Gwamnan zasu karɓi gawar don yi masa Sallah. 

Gwamna Badaru yace za a cigaba da tuna Marigayi Wazirin Dutse da kyawawan halayen sa da kamalar sa da kuma son cigaban al'uma. 

Gwamnan ya kuma miƙa ta'aziyyar sa ga Iyalan Marigayi Mukhtar Muhammad, wanda kuma kafin rasuwar sa shine Shugaban Darektoci na Gidan Rediyo  Freedom kuma Mataimakin Shugaban Dattawan Arewa (ACF) inda yace su ɗauki dangana da tunawa da irin abubuwan alheri da ya shuka a yayin da yake raye. 

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
03/10/2017

No comments: