Adsent

Monday, 2 October 2017

GWAMNA BADARU ABUBAKAR YA BAYYANA RASUWAR AVM MUKHTAR A MATSAYIN BUBBAN RASHI.


Daga Mustee Badala.
Tsinkaya
                Social
                           Network

Gwamna Badaru yayi Jimamin Rasuwar Marigayi Wazirin Dutse; yace Jigawa tayi Rashin Babban Ɗa! Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana rasuwar AVM Mukhtar Muhammad's death a matsayin babban rashi ga jihar Jigawa dama Najeriya baki ɗaya.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya samu labarin rasuwar AVM Mukhtar Muhammad a sanyin safiyar Litinin. Gwamna Badaru yace duk da cewa duk mai rai dole ne ya ɗanɗani mutuwa, amma rashin mutum irin AVM Mukhtar Muhammad babban rashi ne.

AVM Mukhtar Muhammad wanda yake riƙe da Sarautar Wazirin Dutse, tsohon Gwamnan Soji ne na Jihar Kaduna, kuma Shugaban Darektocin Tashar Rediyo mai zaman kanta na farko a Arewa wato Freedom Radio Kano, ya rasu ne a wani asibiti dake birnin Landan bayan yasha fama da rashin lafiya.

Gwamna Badaru yace za a cigaba da tuna Marigayi Wazirin Dutse da kyawawan halayen sa da kamalar sa da kuma son cigaban al'uma. Gwamnan ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya musamman al'umar Jihar Jigawa da su yi koyi da irin halayen sa da ƙoƙarin da yake yi na haɗa kan al'umar ƙasar nan. Gwamnan ya kuma miƙa ta'aziyyar sa ga Iyalan Marigayi Mukhtar Muhammad, inda yace su ɗauki dangana da tunawa da irin abubuwan alheri da ya shuka a yayin da yake raye.

A ƙarshe Gwamna Badaru yace gwamnatin sa zata yi rashin mai bata shawara nagari.

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media (Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)

Mustee Badala
New media Correspondent
02/10/2017

No comments: