Adsent

Monday, 15 May 2017

BAN KWANA DA SABI'U MIKO 'YANDUTSE...

                      TSINKAYA SOCIAL NETWORK...... 


BAN KWANA DA SABI'U MIKO 'YANDUTSE... 

Haƙiƙa dukkanin mai Rai Mamaci ne kamar yadda Allah (swa) ya faɗi a cikin Alƙur' ani mai tsarki,  A yau da misalin ƙarfe goma na safe naga Rubutun Sabi'u Miko yana neman Addu'a domin yana kan hanya zuwa Hadejia. Koda mukayi waya dashi nace masa bana Hadejia da nazo mun gaisa, yace babu damuwa watarana zamu hadu in Allah ya so. Yanzu na samu labarin Rasuwar wannan Bawan Allah dan Gwagwarmaya mai kishin Al'ummar sa, kuma mutum mai fara'a da kamun kai. Hakika Jigawa State Social Media Team munyi rashi sai dai muce Allah ya gafarta masa da rahama ya yafe masa kurakuran sa. 

Sabi'u Miko 'Yandutse mutum ne mai ra'ayi wadda kuma ra'ayinsa bai sanya ya bata da mutane ba, duk rubuce rubucensa a social media bai wuce bayyana ra'ayinsa ba. Allah ya kyauta kwanciya Sabi'u Miko, Allah ya Albarkaci Iyalan da ka bari. 

Sabi'u Miko yana daga cikin waɗanda muka kafa Apc Social media dashi, kuma duk abinda ake na Social media a Jihar Jigawa dashi akeyi, a duk lokacin da yaga anyi Posting wadda bai kamata ba ko a Dandalin Siyasa ko a Apc Social media ko a Tsinkaya, yakan kira na a waya yace in da hali a cire. Kokuma ya min sako ta Inbox a facebook. Allahu Akbar! 

A yau Litinin akan hanyarsa ta komawa gida 'yandutse Hatsarin mota ya rutsa dashi inda ya rasa rayuwarsa. To ba gaggawa yayi ba, muma da muka rage ba jinkiri muka yi ba. Allah yasa mu mutu muna masu imani. 

A madadin ƙungiyar Tsinkaya Social Network ƙarƙashin Jagorancin Habu Badala Gumel, muna meƙa Saƙon Ta'aziyya ga Gwamnatin Jihar Jigawa da Ofishin S. A. New Media Jigawa da Apc Social Media da Crew da sauran Al'ummar Jihar Jigawa, musamman Masarautar Ringim. Muna musu Ta'aziyya Allah ya gafarta masa da rahama ya kyauta makwancin sa Ameen.