
JIHAR JIGAWA, A NIGERIA
***
Hadaddiyar kungiyar yan’kasuwa ta Hadejia ta bayyana gamsuwa bisa kulawar da Gwamnatin jihar jigawa ta nuna sakamakon iftila’in da ya samesu a kwanakin baya, Shugaban kungiyar Malam Bawada Isa ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci shugabannin sauran yan kasuwa zuwa ziyarar godiya ga sakataren zartarwa na hukumar bada agajin gaggawa na jihar Jigawa a ofishinsa.
Malam Bawada Isa ya ce hakan ya nuna yadda Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya damu da jin dadin al’ummar wannan jiha, A nasa jawabin sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji Yusuf Sani Babura yace a koda yaushe burin Gwamnati shine kyautata jin dadin al’umma. Alhaji Yusuf Sani ya ce hukumar ta tallafawa mutane da dama wadanda suka gamu da iftila’i a fannoni daban daban tare da yabawa yan kasuwar bisa wannan ziyarar. Gwamnatin Jihar Jigawa a karkashin Jagorancin Gwamna Badaru Abubakar ta dukufa ne wajen taimakon Al'ummarta, hakan ne yasa Gwamnan yake maida hankali wajen taimakawa masu kananan sana'oi domin dogaro da kai.
Rahoto daga wakilin Tsinkaya
Saifullahi Abbas Hadejia
New Media Correspondent
11/10/2016