Adsent

Sunday, 2 October 2016

DAN MAJALISA SANI ZORRO YA RABA TALLAFI GA JAMA'A. Daga Rabilu S. Kadeta...



Dan majalisar wakilai ta kasa mai wakilai kananan hukumomin Gumel da Maigatari da Suletankarkar da Maigatari Alhaji Muhammad Sani Zorro ya bada tallafin kayayyakin bunkasa tattalin arziki ga mata da maza 150 na mazabarsa.

Kayayyakin tallafin sun hadar da Babura da injunan markade da injunan wuta da kuma kekunan dinki yayinda mata hamsin suka sami tallafin wake da gero da kuma naira dubu uku kowannensu.

A jawabinsa wajen bikin, Alhaji Sani Zorro yace gwamna Badaru Abubakar yana bakin kokarinsa wajen ganin ancigaba da aikin tashar wutar lantarki ta garin Gagarawa.

A jawabinsa shugaban kwamitin riko na KH Gagarawa Alhaji Aminu Sule da shugaban APC na yankin Alhaji Mutari Kale sun bayyana cewar bada kayayyakin ya dace da manufar gwamna Badaru Abubakar na bunkasa tattalin arzikin maza da matan jihar nan

Wadanda suka sami tallafin Shafiu Ubale unguwar Liman da Hajara Liman Mutumbi sun yaba da wannan karamci

Rabilu S. Kadeta
P.R.O
Tsinkaya Social Network Gumel Chapter

No comments: