Adsent

Monday, 10 October 2016

GWAMNATIN JIHAR JIGAWA ZATA HAƊA GWIWA DA KAMFANIN ƘASAR AFIRKA TA KUDU DOMIN SAMAR DA MEGAWAT 80 NA WUTAN LANTARKI




Gwamna Muhammad Badaru Abubakar yace makamashin wutan lantarki yana sa matuƙar tasiri wajen janyo ra'ayin masu zuba jari a Jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne, a yayin da ya karɓi baƙuncin Manajin Daraktan Kamfanin Nova Scotia na Ƙasar Afirka ta Kudu Mr. Amit Modi tare da tawagar sa a gidan Gwamnatin Jihar Jigawa, dake Dutse.

Yace gwamnatin sa ta zagaya sassa daban daban na duniya domin nemo masu zuba jari a Jihar, don haka ake buƙatar tabbataccen wutan lantarki.
Alhaji Badaru Abubakar yace samar da lantarki ta hasken rana zai zama wani madogara ga Jihar domin janyo ra'ayin masu zuba jari a Jihar.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa tasirin da wutan lantarki yake da shi wajen samar da masana'antu ba zai misaltu ba, don haka yace shiri yayi nisa na ƙulla yarjejeniya da kamfanin.

A nasa ɓangaren, Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi, yabawa Gwamnan yayi a ƙoƙarin da yayi na samar da kyakkyawar muhalli ga masu zuba jari a cikin Jihar, inda yace wannan aikin zai taɓa al'uma kai tsaye.
Tun farko a nasa jawabin, Manajin Daraktan Kamfanin samar da wutan lantarki na Nova Scotia, Mr. Amit Modi yace sun kawo ziyarar ne domin sanar da Maigirma Gwamnan irin cigaban da aka samu na gudanar da aikin.
Yace aikin wanda zai samar da ƙarfin wuta mai Megawat 80, zai lashe zunzurutun kuɗi kimanin Dala Miliyan 150.

A yayin da yake gabatarwa Maigirma Gwamnan taswirar aikin, yace za a fara aikin ne a rubu'i na uku na shekara mai zuwa.
A ƙarshe, ya ziyarci Maigirma Gwamnan da ya kai ziyara ƙasar na Afirka ta Kudu domin gane wa idanuwansa makamancin wannan aikin da kamfanin ta gudanar.
Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State On New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
10/10/2016