Adsent

Monday, 9 October 2017

GWAMNA BADARU ABUBAKAR YA GANA DA SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI YAU A ABUJA...





The Governor of Jigawa State Alhaji Muhammad Badaru Abubakar has today meet with President Muhammadu Buhari at his office in the Aso Rock Presidential Villa, Abuja.

The meeting was to brief the President on the achievements recorded by the two Presidential Committees he (Governor Badaru) is chairing as on Fertilizer and Gas and also the Non Oil Revenue. 

Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a yau ya gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Ofishinsa dake Fadar Shugaban Kasa na Aso Rock, Abuja.

An yi ganawar ne domin shi Maigirma Gwamnan yayi wa Maigirma Shugaban Kasar bayanin irin nasarori da cigabanda Kwamituttuka biyu da shi Maigirma Gwamnan ya samu na Samar da Takin Zamani da Iskar Gas da kuma Kwamitin Samar da Kudaden Shiga a hanyoyin da ba na man fetur ba.

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media.

(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
09/10/2017

Thursday, 5 October 2017

GOVERNOR BADARU SWEARS IN NEW PERMANENT SECRETARIES.



Daga Rabilu S Kadeta Da Ibrahim Matafari Kkm. 


The Jigawa State Governor, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar has today sworn-in the newly appointed Permanent Secretaries in Dutse, the state capital.

Speaking shortly after the swearing in, Governor Muhammad Badaru Abubakar said their appointment and subsequent swearing in  to serve the state government in this capacity is purely on merit, competency and personal integrity while he ‎charged them to be fair and just in the discharge of their duties 

The permanent secretaries sworn in are  Sabo Abdu Babura, Sarki Baba Jahun, Lawan Musa Nadada, Ali Garba Dandidi and Murtala Muhammad Kwalam.

The new Permanent Secretaries were administered the Oath of Office and that of allegiance by the Attorney General and Commissioner of Justice Jigawa State Barr. Sani Hussaini Garun Gabas (SAN) 
**************************************************************************
GWAMNA BADARU YA RANTSAR DA SABBIN SAKATARORI NA DINDINDIN 

Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a yau ya rantsar da Sabbin Sakatarori na Dindindin da aka naɗa kwanan nan. 

A yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan rantsuwar, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar yace naɗin su da rantsuwar kama aiki dda aka yi musu anyi ne bisa la'akari da cancantar su, ƙwarewa da ƙwazon su, don haka yayi kira gare su da su zamo masu adalci da tsantseni wajen gudanar da ayyukan su 

Sabbin Sakatarorin na Dindindin ɗin da aka rantsar sune Sabo Abdu Babura, Sarki Baba Jahun da Lawan Musa Nadada, Ali Garba Dandidi da Murtala Muhammad Kwalam.

Sabbin Sakatarorin na dindindin sun karɓi rantsuwar tasu ne daga babban mai Shari'a kuma Kwamishinan Ma'aikatar Shari'a na Jiha Barista Sani Hussaini Garun  Gabas (SAN). 

Auwal D. Sankara (Fica), 
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media 
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa) 
05/10/2017

Wednesday, 4 October 2017

SHUGABA BUHARI YA NADA GWAMNA BADARU YA JAGORANCI YADDA ZA'A TARA DALA BILYAN TALATIN BA TARE DA HARAJIN MAN FETUR BA...

To improve Nigeria’s non-Oil exports, President Buhari appoint Governor Badaru to head Committee as Nigeria targets $30 Billion non-Oil Revenue 

In order to restructure Nigerian economy, the Federal Government is targeting at least $30 billion revenue from non-oil sources; this will be an increase of $25billion from the current $5 billion.

Nigerian Export Promotion Council (NEPC) Director General Segun Awolowo announced the plan after the National Economic Council (NEC) meeting chaired by Vice – President Yemi Osinbajo at the Presidential Villa.

In order to actualize this dream, the Presidency has constituted a committee to come up with a concise action plan on how to drive non-oil exports based on the presentations and discussions at the Economic Council's meeting. 

Awolowo said the objectives of zero oil plan is to add $150 billion to Nigeria foreign reserves in the next 10 years, create 500,000 jobs, lift 10 million Nigerians out of poverty and integrate each state of the federation into the export value chain.

The focus of the plan is on the export of the following crops: rice, wheat, corn, palm oil, rubber, hides and skin, sugar, soya beans and automotive parts among others, and the destination countries for Nigeria’s exports to include Netherlands, China, Iran, Germany, United Kingdom, France, Spain, Italy, India, Saudi Arabia, among others.

Other members of the committee are the Lagos State Governor Akinwunmi Ambode, Ebonyi State Governor Dave Umahi, Ministers of Industry, Trade & Investment, Agriculture & Rural Development, Power, Works & Housing, Transportation and Finance.

Other members are the (NEPC), NEPZA, NEXIM Bank, and the Central Bank of Nigeria (CBN).

The Committee is expected to submit an initial report by November.
**********************************************************************
Domin inganta Kuɗin Shiga daga ɓangarorin da ba na albarkatun mai ba, Shugaba Buhari ya naɗa Gwamna Badaru ya jagoranci Kwamiti da zai samo hanyar da za a tara Dala Biliyan Talatin daga ɓangarorin da ba na Mai ba

Domin sake fasalin tattalin arzikin Najeriya, gwamnatin tarayya ta ƙudurci aniyar samar da aƙalla Dala Biliyan 30 daga ɓangarorin da ba na albarkatun mai ba, wanda hakan zai samar da ƙarin Dala Biliyan 25 daga Dala Biliyan 5 da ake samu a halin yanzu. 

Darekta Janar na Hukumar Bunƙasa Kayayyakin da ake fitar da su Ƙasashen Waje Segun Awolowo ne ya sanar da haka bayan kammala taron Majalisar Tattalin Arziki na Ƙasa wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar Shugaban Ƙasa. 

Domin cimma wannan burin, fadar ta Shugaban Ƙasa ta kafa wani Kwamiti da zai zaƙulo hanyoyin da za a samar da waɗannan kuɗaɗen shiga daga ɓangarorin da ba na albarkatun mai ba, bayan tattaunawa da muhawarori da aka yi yayin taron Majalisar Tattalin Arziki na Ƙasa. 

Awolowo yace an kafa wannan Kwamiti ne a shirin da gwamnati ke yi na daina dogaro da kuɗaɗen shiga da take samu daga albarkatun man fetur da samar wa Najeriya ƙarin kuɗin asusun ƙasa da ƙasa na Dala Biliyan 150 nan da shekaru goma, samar da ayyukan yi ga mutum 500,000, fitar da ƴan Najeriya sama da Miliyan 10 daga ƙangin talauci da kuma baiwa duk wata Jiha damar fitar da kayayyakin da take sarrafawa zuwa Ƙasashen ƙetare. 

Abinda wannan shiri ya sanya gaba shine fitar da kayayyakin masarufi da albarkatun gona da suka haɗa da shinkafa, alkama, masara, Kwakwa, roba, fatu da ƙiraga, sukari, waken soya da kayayyakin motoci da sauran su zuwa Ƙasashen da Najeriya take hulɗar kasuwanci da su irin Holland, Sin, Iran, Jamus, Ingila, Faransa, Andalus, Italiya, India, Saudi Arabia da sauran su. 

Sauran Mambobin Kwamitin sun haɗa da gwamnonin Lagos da Ebonyi wato Akinwunmi Ambode, da Dave Umuahia, Ministocin Masana'antu, Cinikayya da Zuba Jari, Albarkatun Noma da Raya Karkara, Wuta, Ayyuka da Gidaje, Sufuri da Kuɗi. 

Sauran sun haɗa da hukumomin NEPC, NEPZA, Bankin NEXIM, Babban Bankin Najeriya (CBN).

Ana sa ran Kwamitin zata miƙa rahoton ta na farko a watan Nuwamba mai zuwa. 

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
04/10/2017

Tuesday, 3 October 2017

GWAMNA BADARU ABUBAKAR YA ZIYARCI GIDAN MARIGAYI AVM MUKHTAR A YAU.



The Governor of Jigawa State Alhaji Muhammad Badaru Abubakar was this morning among the early callers to pay a condolence visit on the family of Late Wazirin Dutse, Air Vice Marshal Moukhtar Muhammad, former military governor of Kaduna State during the military era. 

Governor Badaru said the late elder statesman epitomizes sincerity and said his wise counsel will be greatly missed.

Late AVM Moukhtar Muhammed, died at London Hospital. His body will arrive Nigeria this evening from England where thousands of sympathizers including the Governor will receive him to pay him their last respect.

The Governor described the late AVM Moukhtar as a man who will be remembered for his sterling qualities of up rightness and selflessness.

The governor condoled with the family of the Chairman of the Board of Directors of Freedom Radio who is also the vice Chairman of Arewa Consultative Forum (ACF), and urged them to take solace in his good deeds and the legacies he left behind.
**********************************************
Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar da sanyin safiyar nan ya ziyarci gidan Iyalan Marigayi Wazirin Dutse Wazirin Dutse, AVM Moukhtar Muhammad, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna a lokacin mulkin soji. 

Gwamna Badaru yace a lokacin rayuwar Marigayin wanda ɗaya ne daga cikin Dattawan ƙasar nan, ya nuna dattaku da gaskiya, kuma za a rasa irin shawarwari masu amfani da ya saba bayarwa. 

Marigayi AVM Moukhtar Muhammed, ya rasu ne a wani asibiti dake Birnin Landan. Ana kuma sa ran gawar sa zai iso Najeriya daga ƙasar Ingila inda dubban jama'a ciki har da Maigirma Gwamnan zasu karɓi gawar don yi masa Sallah. 

Gwamna Badaru yace za a cigaba da tuna Marigayi Wazirin Dutse da kyawawan halayen sa da kamalar sa da kuma son cigaban al'uma. 

Gwamnan ya kuma miƙa ta'aziyyar sa ga Iyalan Marigayi Mukhtar Muhammad, wanda kuma kafin rasuwar sa shine Shugaban Darektoci na Gidan Rediyo  Freedom kuma Mataimakin Shugaban Dattawan Arewa (ACF) inda yace su ɗauki dangana da tunawa da irin abubuwan alheri da ya shuka a yayin da yake raye. 

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
03/10/2017

Monday, 2 October 2017

GWAMNA BADARU ABUBAKAR YA BAYYANA RASUWAR AVM MUKHTAR A MATSAYIN BUBBAN RASHI.


Daga Mustee Badala.
Tsinkaya
                Social
                           Network

Gwamna Badaru yayi Jimamin Rasuwar Marigayi Wazirin Dutse; yace Jigawa tayi Rashin Babban Ɗa! Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ya bayyana rasuwar AVM Mukhtar Muhammad's death a matsayin babban rashi ga jihar Jigawa dama Najeriya baki ɗaya.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya samu labarin rasuwar AVM Mukhtar Muhammad a sanyin safiyar Litinin. Gwamna Badaru yace duk da cewa duk mai rai dole ne ya ɗanɗani mutuwa, amma rashin mutum irin AVM Mukhtar Muhammad babban rashi ne.

AVM Mukhtar Muhammad wanda yake riƙe da Sarautar Wazirin Dutse, tsohon Gwamnan Soji ne na Jihar Kaduna, kuma Shugaban Darektocin Tashar Rediyo mai zaman kanta na farko a Arewa wato Freedom Radio Kano, ya rasu ne a wani asibiti dake birnin Landan bayan yasha fama da rashin lafiya.

Gwamna Badaru yace za a cigaba da tuna Marigayi Wazirin Dutse da kyawawan halayen sa da kamalar sa da kuma son cigaban al'uma. Gwamnan ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya musamman al'umar Jihar Jigawa da su yi koyi da irin halayen sa da ƙoƙarin da yake yi na haɗa kan al'umar ƙasar nan. Gwamnan ya kuma miƙa ta'aziyyar sa ga Iyalan Marigayi Mukhtar Muhammad, inda yace su ɗauki dangana da tunawa da irin abubuwan alheri da ya shuka a yayin da yake raye.

A ƙarshe Gwamna Badaru yace gwamnatin sa zata yi rashin mai bata shawara nagari.

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media (Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)

Mustee Badala
New media Correspondent
02/10/2017

Sunday, 1 October 2017

DAGA MA'AIKATAR LAFIYA TA JIHAR JIGAWA.


JIGAWA STATE MINISTRY OF HEALTH

Gwamnatin jihar jigawa karkashin jagorancin gwamna Badaru Abubakar,  ta fitar da sabon jadawalin bada abinci a manyan  asibitocin jihar nan ga marassa lafiya.
Kwamishinan lafiya Dr.Abba Zakari ya bada umarnin sake fasalin sabon jadawalin domin dacewa da yanayin samun saukin marassa lafiya.

Kwamishinan ya Kara da Cewa jadawalin ya fara aiki daga Yau 01 October 2017 kuma ana sanar da al'umma duk Wanda ya tarar sabanin abin da yake jadawalin ka kira 07038379934, 07065934753.

Gwamnatin ta jihar Jigawa tana bada fifiko ga bangaren lafiya, sakamakon Lafiya itace gaba da komai, Kwamishinan Lafiya Dr. Abba ya kware wajen Inganta harkar lafiya domin daga zamansa Kwamishina ma'aikatar lafiya ta samu kyawawan tsare tsare don inganta lafiya. 

Rahoto daga Rabilu S Kadeta
Chairman Tsinkaya Social Network Gagarawa Chapter