Adsent

Monday, 26 September 2016

ZA'A KEWAYE DUKKANIN MAKARANTUN PRIMARY DA KANANAN MAKARANTUN SAKANDIRE NA JIHAR JIGAWA. Daga Yahya Salisu Gabari.



Hukumar ilmi a matakin farko ta jihar Jigawa tace tana shirye shiryen kewaye makarantun firamare da kananan makarantun sakandaren
jihar nan domin kare su daga cin kan iyaka, Shugaban hukumar Alhaji Salisu Zakar ya bada tabbacin haka a lokacin da shugabannin kwamitin kula da harkokin ilmi na makarantun Kafin Hausa Mallam Madori suka ziyarci ofishinsa.

Shugaban Yace gwamnatin jiha tana yin dukkan abinda ya dace wajen kyautata yanayin koyo da koyarwa a makarantun jihar nan, tare da
alkawarin duba bukatun da suka gabatar. Alhaji Salisu Zakar ya yaba da irin gudunmawar da kwamitocin kula da harkokin ilmi na makarantu ke bayarwa wajen hana cin iyakokin makarantu. Tunda farko dai wakilin shugaban kwamitin Alhaji Abubakar Hassan ya shaidawa shugaban
hukumar cewar sun kawo ziyarar ne domin neman gina musu karamar sikandaren Arabiyya a unguwar shagari, sakamakon yawan jama'a da yankin yake dashi.

No comments: