Adsent

Sunday, 25 September 2016

GWAMNA BADARU ABUBAKAR YA KAI ZIYARAR TA'AZIYYA KANYA BUBBA.


Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) a yau ya tafi garin Kanya Babba dake Ƙaramar Hukumar Babura domin ta'aziyyar matasa goma sha biyu da suka rasa rayukansu.

Matasan sun rasu ne sanadiyyar haɗarin mota da ya rutsa dasu a hanyar su ta zuwa Jihar Legas, bayan Bikin Babban Sallah.

Gwamna Muhammad Badaru ya je ta'aziyyar ne a fadan Maigirma Hakimin Kanya Babba kuma Makaman Ringim Alhaji Muhammadu Ibrahim.

Gwamna Badaru yace rasa waɗannan matasa abun alhini ne, kuma ba wai rashi ne ga al'umar Kanya Babba ko Ƙaramar Hukumar Babura kaɗai, yace babban rashi ne ga ɗaukacin al'umar Jihar Jigawa.

Gwamnan yace yana kyautata zaton mamatan suna cikin rahama, saboda sun rasa rayukansu ne a madaidaiciyar hanya, ta neman halak.

Gwamna Badaru yayi addu'ar Allah ya jikan mamatan, ya kuma bawa waɗanda suka samu raunuka lafiya, ya kuma bawa iyalan mamatan haƙurin jure wannan Babban Rashi.

A jawabinsa, Maigirma, Makaman Ringim kuma Hakimin Kanya Babba Alhaji Muhammadu Ibrahim ya godewa Maigirma Gwamnan da wannan ziyarar ta'aziyyar da ya zo musu, inda yace wannan hali ne na Shugaban da ya damu da al'umar sa.

A nan Hakimin yayi addu'ar Allah ya maida Maigirma Gwamnan da ƴan tawagar sa gida lafiya, ya kuma basu ladan ta'aziyya.

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
25/09/2016

No comments: