Adsent

Tuesday, 27 September 2016

DAGA MAJALISSAR JIHAR JIGAWA.. Rahoton Isah Ramin Hudu.



Majalissar dokokin Jihar Jigawa ta amince da karin wa'adin watanni Shida ga Shugabannin Kwamitotin riko na kananan hukumomin Jihar 27, Shugaban majalisaar Hon. Idris Garba Jahun ne, ya sanarda hakan a zaman majalissar na yau bayan dawowarsu daga hutun Babbar Sallah.

Tunda farko dai Dan majalissar Dokokin jiha mai wakiltar Mazabar Kazaure Hon. Barr. Yusuf Gada wadda shine mataimakin bulaliyar majalissar ya gabatar da kudirin Karin wa'adin watanni Shidan, abisa tanadin Sashe na 7 na dokar kananan hukumomin jihar jigawa.
Daga nan kudirin yasamu goyon bayan Dan majalissa mai wakiltar Mazabar Bulangu, Hon. Abudullahi Muhammad Toyin.

Muna Adduar Allah Ya Kara Tayasu Riko. Ya Cigaba Da Taimakon Gwamnatin Muhammadu Badaru Abubakar (Kadimul Islam) Da Mataimakinsa Barr. Ibrahim Hassan Hadejia.

No comments: