

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa ya Halarci ziyarar ta'aziyya ga iyalan tsohon Sanatan Jigawa ta Arewa maso Yamma, Sanata Dalha Danzomo, a gidan sa dake Unguwar Hotoro, a jihar Kano.
Tsohon Sanatan wanda ya rasu a daren jiya an yi masa sutura a yau da binne shi kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar. Gwamna Muhammad Badaru yace tsohon Sanatan mai kishin ƙasa ne kuma gogaggen ɗan Siyasa wanda ya bautawa al'umarsa tuƙuru. Daga nan yayi masa addu'ar samun rahama, ya kuma baiwa iyalansa haƙurin jure rashin.
A wani labari makamancin wannan, Gwamna Muhammad Badaru ya kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan tsohon Babban Mai Shari'a na Ƙasa, Mai Shari'a Dahiru Mustapha, wanda yayi rashin ƙanwarsa Hajiya Hafsatu Mustapha. Gwamnan yayi addu'ar Allah yayi mata rahama, ya kuma baiwa iyalanta haƙurin jure wannan Babban Rashi.
Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
28/09/2016