In continuation of his inspections to health Facilities and other projects within the state, the Governor of Jigawa State Alhaji Muhammad Badaru Abubakar has today inspected the Kazaure General Hospital, Psychiatric Hospital and also the land allocated for the construction Specialist Hospital.
Governor Badaru called on the contractors handling the project of the construction of the specialist hospital to speed up work in order to meet up with the time alloted for the project, while at the psychiatric hospital, Governor Badaru promised that his administration will equip the psychiatric hospital in order to better the living standard and welfare of the inmates.
Governor Badaru also inspected the on-going Kazaure Township Roads and drainages being constructed in the Emir's Palace Road.
Governor Badaru also visited Primary Healthcare Centers in Roni, Gwiwa, Yankwashi before proceeding to Government Science Secondary School Kanya Babba in Babura Local Government.
At the GSSS Kanya Babba, after listening to the pleas of the school management on lack of portable water, promised to come to their aid as soon as earnest.
****************************************
A cigaba da ziyarar da yake kaiwa cibiyoyin lafiya da wasu muhimman ayyuka a faɗin Jiha, Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar a yau ya kai ziyarar gani da ido a Babban Asibitin garin Kazaure, Asibitin Mahaukata na Kazaure da duba filin da aka ware domin gina Asibitin Ƙwararru na Kazaure.
Maigirma Gwamnan yayi kira ga ƴan kwangilar dake aikin Asibitin Ƙwararrun da su hanzarta kammala aikin a lokacin da aka ƙayyade musu, a inda kuma a ziyarar da ya kai asibitin Mahaukata yayi alƙawarin cewa gwamnatin sa zata gyara asibitin domin inganta kula da lafiyar majinyatan.
Duk a cikin garin Kazaure, Gwamna Badaru ya duba ayyukan titunan cikin gari da ake yi a halin yanzu, tare da duba magudanan ruwa da ake yi a wajen ƙofar Fadar Kazaure.
Gwamna Badaru ya kuma kai ziyara ɗakunan sha magani na sha ka tafi na garuruwan Roni, Gwiwa, da Yankwashi kafin ya zarce zuwa Makarantar Sakandiren Kimiyya na Kanya Babba dake Ƙaramar Hukumar Babura.
A Sakandiren Kimiyyar na Kanya Babba, bayan jin ƙorafin hukumar makarantar na rashin ruwa, Maigirma Gwamnan yayi alƙawarin kawo masa ɗauki cikin gaggawa.
Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
25/09/2017