Adsent

Monday, 15 May 2017

BAN KWANA DA SABI'U MIKO 'YANDUTSE...

                      TSINKAYA SOCIAL NETWORK...... 


BAN KWANA DA SABI'U MIKO 'YANDUTSE... 

Haƙiƙa dukkanin mai Rai Mamaci ne kamar yadda Allah (swa) ya faɗi a cikin Alƙur' ani mai tsarki,  A yau da misalin ƙarfe goma na safe naga Rubutun Sabi'u Miko yana neman Addu'a domin yana kan hanya zuwa Hadejia. Koda mukayi waya dashi nace masa bana Hadejia da nazo mun gaisa, yace babu damuwa watarana zamu hadu in Allah ya so. Yanzu na samu labarin Rasuwar wannan Bawan Allah dan Gwagwarmaya mai kishin Al'ummar sa, kuma mutum mai fara'a da kamun kai. Hakika Jigawa State Social Media Team munyi rashi sai dai muce Allah ya gafarta masa da rahama ya yafe masa kurakuran sa. 

Sabi'u Miko 'Yandutse mutum ne mai ra'ayi wadda kuma ra'ayinsa bai sanya ya bata da mutane ba, duk rubuce rubucensa a social media bai wuce bayyana ra'ayinsa ba. Allah ya kyauta kwanciya Sabi'u Miko, Allah ya Albarkaci Iyalan da ka bari. 

Sabi'u Miko yana daga cikin waɗanda muka kafa Apc Social media dashi, kuma duk abinda ake na Social media a Jihar Jigawa dashi akeyi, a duk lokacin da yaga anyi Posting wadda bai kamata ba ko a Dandalin Siyasa ko a Apc Social media ko a Tsinkaya, yakan kira na a waya yace in da hali a cire. Kokuma ya min sako ta Inbox a facebook. Allahu Akbar! 

A yau Litinin akan hanyarsa ta komawa gida 'yandutse Hatsarin mota ya rutsa dashi inda ya rasa rayuwarsa. To ba gaggawa yayi ba, muma da muka rage ba jinkiri muka yi ba. Allah yasa mu mutu muna masu imani. 

A madadin ƙungiyar Tsinkaya Social Network ƙarƙashin Jagorancin Habu Badala Gumel, muna meƙa Saƙon Ta'aziyya ga Gwamnatin Jihar Jigawa da Ofishin S. A. New Media Jigawa da Apc Social Media da Crew da sauran Al'ummar Jihar Jigawa, musamman Masarautar Ringim. Muna musu Ta'aziyya Allah ya gafarta masa da rahama ya kyauta makwancin sa Ameen. 

Tuesday, 11 October 2016

YAN’KASUWA NA HADEJIA SUN YABAWA GWAMNATIN SARDAUNA/SHETTIMA.. Daga Saifullahi Abbas Hadejia.



JIHAR JIGAWA, A NIGERIA
***

Hadaddiyar kungiyar yan’kasuwa ta Hadejia ta bayyana gamsuwa bisa kulawar da Gwamnatin jihar jigawa ta nuna sakamakon iftila’in da ya samesu a kwanakin baya, Shugaban kungiyar Malam Bawada Isa ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci shugabannin sauran yan kasuwa zuwa ziyarar godiya ga sakataren zartarwa na hukumar bada agajin gaggawa na jihar Jigawa a ofishinsa.

Malam Bawada Isa ya ce hakan ya nuna yadda Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar ya damu da jin dadin al’ummar wannan jiha, A nasa jawabin sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji Yusuf Sani Babura yace a koda yaushe burin Gwamnati shine kyautata jin dadin al’umma. Alhaji Yusuf Sani ya ce hukumar ta tallafawa mutane da dama wadanda suka gamu da iftila’i a fannoni daban daban tare da yabawa yan kasuwar bisa wannan ziyarar. Gwamnatin Jihar Jigawa a karkashin Jagorancin Gwamna Badaru Abubakar ta dukufa ne wajen taimakon Al'ummarta, hakan ne yasa Gwamnan yake maida hankali wajen taimakawa masu kananan sana'oi domin dogaro da kai. 

Rahoto daga wakilin Tsinkaya
Saifullahi Abbas Hadejia
New Media Correspondent
11/10/2016

BANKIN ZENITH TA BAIWA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA KYAUTAR MOTAR BAS MAI CIN MUTUM 16...

ZENITH BANK DONATES 16 SEATER BUS TO JIGAWA STATE GOVERNMENT..




Zenith Bank Nigeria Plc has adopted Dutse Model International School for its Educational Intervention Programme. The Bank Zonal Manager Alhaji Umar Ahmad stated this when he paid a Courtesy Visit to Governor Muhammad Badaru Abubakar at the Government House.
He explained that this year, the Bank supported ten (10) best students selected from the Jigawa State Public Schools with Two Hundred and Fifty Thousand Naira (N250, 000.00) each as scholarship grant, in an effort to encourage them in their educational pursuit.

Alhaji Umar Ahmad pointed out that in an effort to ease official mobility; the bank donated 16 Seater Bus to Jigawa State Government as part of their Corporate Social Responsibility.
Responding, Governor Muhammad Badaru Abubakar expressed his appreciation for the visit and also thanked the management of the bank for the gesture.

He noted that the Bank and the State Government have a long cordial relationship, while urging the bank to continue with the laudable efforts.


Bankin Zenith ta zaɓi makarantar Dutse Model International School domin gudanar da shirinta na tallafawa harkar ilimi. Manajan Shiyya na Bankin Alhaji Umar Ahmad shi ya bayyana haka a yayin da ya kawowa Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar ziyara a Gidan Gwamnati. Ya bayyana cewa, a wannan shekarar na 2016, Bankin ta zaƙulo hazikan Ɗaliban makarantun sakandare guda goma daga makarantun gwamnati dake Jihar Jigawa, inda ta tallafawa kowannensu da kuɗi Naira Dubu Ɗari Biyu Hamsin (N250, 000.00) domin ƙarfafa musu gwiwa a harkar karatunsu.

Alhaji Umar Ahmad ya nuna cewa domin rage wa bangaren gwamnatin wahalhalu ta ɓangaren sufuri ne, yasa bankin taga dacewar bayar da gudunmawar Mota ƙirar Bas mai cin mutum 16. A jawabinsa, Gwamna Muhammad Badaru ya bayyana farin cikin sa da wannan ziyara da suka kawo masa tare da yin godiya ga bankin da wannan gudunmawa da suka bayar. Ya nuna cewa Bankin da Gwamnatin Jihar Jigawa suna da kyakkyawar alaƙa tun baya, inda ya bukace su, su ci gaba da tabbatar da wannan alaƙa.

Auwal D. Sankara (Fica),
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
11/10/2016