Adsent

Monday, 27 June 2016

MA'AIKATAR GONA.... By Aminu Ali.



Ma'aikar Gona Ta Jihar Jigawa Ta Kafa
Committee Mai Wakilai Mutum Bakwai (7)
Domin Bullo Da Yadda Za'a fara Safarar
Dabbobin Gida Daga Jihar Jigawa Zuwa
Kasar Saudiyya. Dabbobin Da Za ayi Safarar Tasu sun Hada da shanu, Rakuma, Akuyoyi da kuma Tinkiyoyi.
Commissioner Ma'aikatar Gona Ta Jihar
Jigawa Alh Kabiru Ali ne Ya Bayyana
Hakan Ayayin da Yake Kaddamar da
Kwamitin a Office Dinsa Alh Kabiru Ali
Yace Makasudin wannan kwamiti shine Ya lalumo Dabbobin Da Za'a dinga Safararsu Kwamishinan Shine Wanda Zai Kula Da Shirin Domin Ganin Anyi Aiki Ba Dare Ba Rana Domin Tabbatuwar Ansamu Nasarar Shirin Kwamitin Wanda Dr Salisu Abdullahi Yake A Matsayin Shugaba da kuma Bashir Abdu Ringim a Matsayin Secretary sauran yan Kwamitin Sunhadar da Mal Idris Isyaku da Abdullahi Sunusi da Muhammad Idris.

Dayake Magana a Matsayinsa na Chairman din Kwamiti Dr Salisu Abdullahi
Yayi Alkawarin Bada Tabbacin Gaskiya da
Rikon Amana Bisa Wannan Aiki da Aka
Doramusu.
***
Aminu Ali
Tsinkaya social network.

posted from Bloggeroid

No comments: