The Executive Governor of Jigawa State Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) has today attended the commissioning of Juma'at Masjid (Mosque) at Tsauni Village of Wurno town in Birnin Kudu Local Government.
In his sermon, the chief Imam of the mosque, Ustaz Bayero Jigawar Sarki admonished people to seek for knowledge.
He said it is only with adequate Islamic knowledge that one can worship Allah as enshrined in the holy Qur'an and the Hadith of the Prophet.
The Imam enjoined Muslims to assist the less privileged in the society especially in this month of Ramadan.
He concluded the sermon with offering prayers for peace and development in the State and Country at large.
Also in attendance in the Commissioning Ceremony were the Honourable Minister of Water Resources Alhaji Sulaiman Adamu, Deputy Governor Barr. Ibrahim Hassan Hadejia, Emir of Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi, Senator Sabo Muhammad Nakudu, Senator Abdul Ningi, APC Chieftain Farouq Adamu Aliyu, Secretary to the State Government, Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini, Member Representing Birnin Kudu/Buji Magaji Da'u Aliyu, some Commissioners, Special Advisers and Special Assistants as well as other Muslim Ummah.
**
Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) a yau ya halarci taron bude Masallacin Jumu'a dake Kauyen Tsauni na garin Wurno a Karamar Hukumar Birnin Kudu.
A hudubarsa, Babban Limamin Masallacin Jumu'ar Ustaz Bayero Jigawar Sarki yayi kira ga jama'a da su dage da neman ilimi.
Yace sai da ilimin addini ne kadai Dan Adam zai bautawa Allah kamar yadda Kur'ani da Hadisai suka kawo.
Babban Limamin ya kuma yi kira da a rika taimakawa marasa karfi musamman a wannan wata mai albarka na Ramadan.
A karshe Limamin yayi adfu'ar zaman lafiya da cigaba ga Jiha da Kasa baki daya.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Ministan Albarkatun Ruwa Alhaji Sulaiman Adamu, Mataimakin Gwamnan Jiha Barista Ibrahim Hassan Hadejia, Mai Martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammad Sunusi, Sanata Sabo Muhammad Nakudu, Sanata Abdul Ningi, Jagoran Jam'iyar APC Farouq Adamu Aliyu, Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini, Wakilin Tarayya na Birnin Kudu/Buji Magaji Da'u Aliyu, Kwamishinoni, masu bada shawara da mataimaka na musamman da sauran al'ummah.
Auwal D. Sankara,
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
17/06/2016
posted from Bloggeroid