

The Executive Governor of Jigawa State Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar (MON, mni) on Thursday received the members of Malam Madori Youth Concern Development at his office in Jigawa State Government House, Dutse.
The members said they were at the Government House to felicitate with him over his victory at the polls and thank him for the support he rendered to one of their ailing member. The association also request the Executive Governor
to provide some basic amenities to the community.
The Governor commended them for their contributions and said plan is under way to construct township in Malan Madori despite the dwindling revenue in the state and the country.
The Governor noted that as a result of shrinking of the revenue the state maintain its status in paying its salary, and as at now the government had awarded the rehabilitation of water schemes in the state. In a related development, the Executive Governor also received the delegation of APC
Fulde Forum; a political group of Miyetti Allah Organization, for the second time after being sworn in as the Executive Governor of Jigawa
State and to intimate him on the forthcoming Miyetti Allah Organisation Election in Jigawa
State. The visitors said they were at the Governor's Office to reaffirm their absolute loyalty and assured him of their unflinching support to the administration.
Governor Badaru welcomed them and promised to support them to conduct a hitch free election.
Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) a ranar Alhamis ya karbi bakuncin Kungiyar Cigaban Matasa ta Karamar Hukumar Malam Madori a ofishinsa dake gidan Gwamnatin Jihar Jigawa. Bakin sun sanar da Maigirma Gwamnan cewa makasudin kawo ziyarar shine don su taya shi farin ciki nasarar da ya samu, su kuma mika godiyar su gareshi bisa taimakon da yayi wa
daya daga cikin dan kungiyar su wanda ya kwanta rashi lafiya sa'annan su roki gwamnati da ta samar da ababen more rayuwa a karamar hukumar ta Malam Madori.
Gwamnan ya yaba musu akan irin gudunmuwar da suke bayarwa, tare da tabbatar musu da cewa duk da yanayin tattalin arziki amma anyi
tsarin yin ayyukan cigaba a garin Malam Madori.
Gwamnan yace duk da yanayin koma bayan tattalin arzikin kasa kuma ya shafi Jihar Jigawa,gwamnati ta cigaba da biyan albashi kuma a
yanzu gwamnati ta bada damar a gyara ma'aikatar ruwa a jihar.
A daya gefen kuma, Kungiyar Fulde na APC ne suma suka kawo nasu ziyarar a Karo na biyu bayan rantsar da Gwamna a matsayin Gwamnan
Jihar Jigawa domin kara jaddada goyon bayan su da sanar dashi zaben da kungiyar Miyetti Allah
ke shirin yi. Gwamnan yayi maraba da zuwansu inda ya tabbatar musu da shiga cikin al'amuran nasu domin yin zabe cikin kwanciyar hankali.
Auwal D. Sankara,
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa A Sabbin Kafafen Sadarwa)
06/11/2015
No comments:
Post a Comment