Adsent

Saturday, 7 November 2015

GWAMNATIN NIGERIA ZATAYI KASAFIN KUDIN SHEKARAR 2016...

Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce aiki yayi nisa yanzu wajen shirya gagarumin kasafin kudi na shekarar 2016, wanda ake gani zai kai har kimanin naira triliyan bakwai 7 zuwa takwas 8. Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ne ya yi tsokacin a wajen taron bitar da aka shiryawa sabin ministocin kasar 36. Kasafin kudin kasar da aka shirya na shekarar 2015, naira triliyan hudu ne da doriya, saboda haka, a kasafin na badi, za'a samu gagarumin karin kudade.

Gwamnatin dai ta shirya aiwatar da gagarumin kasafin ne a daidai lokacin da kasar ke fama da
rashin kudi. Mallam Garba Shehu, kakakin shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatin ta na so ta ware fiye da kashi 40 cikin dari domin gudanar da manyan ayyuka, sabanin a baya yadda aka ware kimanin kashi 70 cikin dari ga ayyuka yau da kullum.

Ya ce gwamnati za ta nemo kudaden ne ta hanyar karbar haraji yadda ya kamata, da kuma wani asusu na hadin gwiwa da bangarori masu
zaman kansu.



No comments: