
Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) yace rashin Nasiru Habu Babura babban rashi ne ba wai ga Iyalansa kadai, rashi ne ga daukacin al'umar Jihar Jigawa,musamman yan jam'iyyar APC.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya ziyarci gidan iyalan Marigayin a garin Babura domin yi musu ta'aziyar wannan rashin.
Marigayin wanda Allah ya masa rasuwa ranar Juma'a da ta gabata shine Shugaban Kungiyar APC Social Media na Jihar Jigawa.
Labarin rasuwar ya riski Maigirma Gwamna ne a yayinda yake wajen taron bita a Kaduna inda tun a can ya bayyana alhininsa da wannan babban rashi ga Iyalan mamacin, al'umar Karamar Hukumar Babura da Jihar Jigawa.
Gwamnan yace halayen mamacin kyawawa ne abun koyi kuma ya bayar da gudunmawa mai yawa musamman a lokacin zabensa na
Gwamnan Jihar Jigawa musamman a shafukan sada Zumunta. Kamar yadda Gwamnan yace "Rayuwar Nasiru Habu ya taba mutane da yawa, kuma yana da masoya da yawa, shi yasa rasuwar sa ya taba
mutane da dama a garin Babura da Jihar Jigawa musamman a shafukan sada Zumunta".Gwamnan yayi addu'ar Allah ya jikan mamacin,
ya kuma yi masa sakayya da gidan Aljanna. Gwamnan yayi amfani da damar domin yin wasu ta'aziyar a garin na Babura inda ya fara da
gidan tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Jigawa Alhaji Adamu Dan Gile Babura wanda ya rasa mahaifiyar sa.
Sannan ya kai wasu ta'aziya a gidan Malam Abdullahi Gumal Babura da gidan Malam Danazimi Odar Babura da kuma gidan Hajiya Ma'u Yakubu Babura.
Auwal D. Sankara, Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State On New Media.
posted from Bloggeroid