Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa kuma Dan takarar gwamna Mallam Umar Namadi ya kada kuri'ar sa a mazabar sa, dake karamar hukumar Kafin Hausa. Da yake jawabi bayan kammala zaben ya bukaci jama'a da ayi zabe cikin lumana da kwanciyar hankali, ya kuma bukaci matasa da a kai zuciya nesa domin mai Nasara baya fada.
Zabe dai a jihar jigawa ana yin sa cikin kwanciyar hankali da lumana, babu wani rahoto da ya nuna an samu rikici ko fasa Akwatin zabe. Tun farko dai jam'iyyar mai mulki a jihar wato Apc ta yi kira ga 'ya'yan ta da su guji duk wata fitina da zata kawo Tashin hankali ko janyo abinda zai kawo rashin zaman lafiya.
No comments:
Post a Comment