31-05-2017 RADIO
Gidan redion Jigawa da sauran tashoshin FM zasu gabatar da muku da shiri na musamman kan alamurran siyasar jihar nan cikin shekaru biyu na mulkin gwamna Badaru Abubakar shirin zai zo muku ne da misalin karfe tara na daren yau zuwa tara da minti arbain da biyar sannan a maimata shirin a gobe alhamis da misalin karfe tara da rabi na safe zuwa goma da minti goma sha biyar na safe
31-05-2017 BIRNIN KUDU
An kaddamar da sabbin shugabannin majalissar matasa ta K. H Birnin Kudu. Wadanda aka kaddamar sun hadar da Comrade Sanusi Idris shugaba da Kabiru Garba Wurno mataimakin shugaba da Maharazu Umar Maaji da Abdulrazak Muhammad sakataren kudi da Auwal Iiliyasu PRO da kuma Haruna Isa sakataren majalissar.
A jawabinsa wajen bikin kaddamar da shugabannin majalisar Matasan, mataimakin na musamman ga gwamna kan harkokin matasa Alhaji Salisu Rabiu Babura ya nanata kudirin gwamnati na samarwa matasa hanyoyin dogaro da kai a bangarori daban daban. A jawabinsa shugaban kwamitin riko na yankin Mallam Adamu Garba ya yi alkawarin bada ofishi ga majalissar.
Ya kuma bukaci matasan dasu guji shan miyagun kwayoyi da munanan dabiu. A jawabinsa na godiya shugaban majalissar Comrade Sanusi Idris yace majalissar itace lemar duk wata kungiya ta matasa a kasar nan Daga bisani dan majalissar wakilai ta kasa Injiniya Magaji Dau ALiyu ya baiwa majalisar gudunmawar naira dubu hamsin.
An yi kira gay an kwangila dake gudanar da aikin gyaran masalatan jumaa na garuruwan Kiyawa da Katanga dasu maida hankali wajen kammala aikin akan lokaci. Shugaban kwamitin riko na yankin Abdullahi Suleiman Yayari ya yi bukatar a lokacin ziyarar gani da ido. Yace KH ta biya sauran kason kudin aikin da ya rage domin baiwa yan kwangilar damar kammala aikin akan lokaci. Alhaji Abdullahi Suleiman ya yi fatan zasu gudanar da aiki mai inganci.
31-05-2017 HADEJIA
Mai martaba sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Hadejia ya bude karatun tafsir na watan Ramadan a gidan kurkuku na Mawadaci. A jawabinsa mai martaba sarki ya bukaci masu abin hannu dasu tallafawa wadanda suke zaune a gidaje yari domin tallafawa rayuwarsu Ya ce mazauan gidajen yari suna bukatar tallafi Sarkin ya kuma duba irin kayayyakin da daurarru suke sarrafawa.
A jawabinsa wakilin shugaban gidan yari na jiha ASP Adam Muhammad Bello ya yabawa sarkin bisa damuwarsa ga gidan yarin.
31-05-2017 TAKUR
An yi kira ga hukumar gidaje ta jihar Jigawa da ta yashe magudanan ruwa da kwalbatoci a unguwar Takur domin gudun ambaliyar ruwa. Mazauna unguwar sun bayyana cewar sakamakon mamakon ruwan saman da aka gudanar a wannan rana , layuka da kuma gidaje da dama sun cika da ruwa makil sakamakon cikewar magudanan ruwan da kwalbatocin unguwannin suka yi. Wani magidanci Mallam Musa ya ce ruwan ya mamaye layinsu ta yadda sai mutum ya tattare wando yake samun hanyar fita.
Daga nan sai ya bukaci hukumar data taimaka wajen yashe magudanan ruwan domin gudun ambaliyar ruwa. Haka zalika suma mazauna unguwar gida dubu yadin dutse sun roki hukumar gidaje ta jiha data kai musu dauki ta yadda wasu layukan ke cika da ruwan sama da zarar an samu mamakon ruwa. wani mazaunin unguwar Mallam Anas yace muddin aka yi ruwa to suna fargaba shiga gidajen su musamman mazauna layin dibinai.
31-5-2017 BUJI
Shirin yaki da yunwa na majalisar dinkin duniya a karamar hukumar Buji ya raba kudi naira miliyan talatin da tara ga mata masu juna biyu da kananan yara dubu tara da dari biyu da casa’in da tara.
Jami’in kula da shirin a karamar hukumar,Malam Abdullahi Muhammad ya bayyana haka lokacin taro da kwamatin masu ruwa da tsaki na yankin. Ya ce tuni aka ya yaye mata dari tara da biyar wadanda suka ci gajiyar shirin na tsawon watanni talatin, inda ya bukace su su yi kyakkyawan amfani da kudaden da aka ba su.
31-5-2017 GWARAM
Karamar hukumar Gwaram ta tallafawa yan asalin yankin wadanda zasu tantancewar shiga aikin soja kimanin saba’in da takwas da kudin mota da kuma na abinci. Shugaban kwamatin riko na karamar hukumar Alhaji Umar Illu Shuwarin ya bayyana haka lokacin da yake jawabin ban kwana ga matasan a sakatariyar karamar hukumar.
Ya bukace su, su kasance masu juriya da zama jakadu na gari wajen karbar horon aikin soja. Shugaban wanda ya sami wakilcin sakataren karamar hukumar Alhaji Yakubu Abdullahi ya ce a shirye suke su tallafawa dukkanin dan asalin yankin da ya sami wata dama ta samun aiki musamma a matakin tarayya.
31-5-2017 LAFIYA
Gwamnatin jihar Jigawa ta bude tayin bada kwangilar aikin gina sabon asibitin kwararru a garin Hadejia. Da yake jawabi a wajen bude bada tayin kwangilar, kwamishinam lafiya na jiha, Dakta Abba Zakari ya ce gwamnati ta kudiri niyyar gina sabon asibitin kwararrun ne domin maye-gurbin asibitin kwararru na Reshid Shekoni wanda jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutse ta karba domin mayar da shi asibitin koyarwa.
Dakta Abba Zakari ya ce gwamnatin jiha ta damu da ganin ta fadada ayyukan kwararru a fanin kiwon lafiya zuwa kowane loko da sako na jihar nan. Ya ce kamfanoni fiye da ashirin ne suka nuna sha’awarsu ta neman kwangilar, inda daga bisani biyar daga cikinsu suka cancanta , yayin da suka gabatar da takardunsu ga kwamatin tantance kamfanonin.
A jawabinsa babban sakataren ma’aikatar lafiya, Dakta Muhammad Abdullahi ya bukaci kamfanonin da zasu yi nasara su tabbatar sun gudanar da aiki mai inganci. Daya daga cikin wakilan kamfanonin kuma wakilin kamfanin PACHE-NIG LTD, Sakkis Abi ya bada tabbacin yin aiki mai kyau da zarar sun sami nasara.
31-5-2017 RUWA
Ma’aikatar albarkatun ruwa ta jihar Jigawa ta bude tayin bada kwangilar haka rijiyoyin tuka-tuka dari da talatin da shida a mazabu yan majalisar dokokin jiha talatin. Da yake jawabi wajen bude tayin bada kwangilar, Kwamishinan ma’aikatar Alhaji Ibrahim Garba Hannun-Gwiwa ya ce an ware fiye da naira miliyan dari da ashirin da uku domin gudanar da aikin.
Kwamishinan wanda ya sami wakilcin manajan daraktan hukumar samar da ruwan sha a matsakaitan garuruwa, Injiniyya Labaran Adamu ya ce kamfanoni hamsin da daya ne suka shiga tayin bada kwangilar, inda ya bukaci kamfanonin da suka sami nasara su yi aiki mai inganci.
A jawabinsa wakilin kamfanonin da suka sami nasara Alhaji Ma’azu Ma’zau ya yi alkawarin yin aiki mai kyau da kuma inganci.
31-5-2017 YUGUDA
An yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa aniyarta na gina hanyar Gwaram zuwa Basirka a yankin karamar hukumar Gwaram. Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar karamar hukumar, Alhaji Yuguda Hassan Kila ya yi wannan yabo, jim kadan da kaddamar da gadar Sagi dake kan hanyar Gwaram zuwa Basirka.
Wakilinmu Muhammad Sabo Kila nada karin bayani...
Alhaji Yuguda Hassan Kila wanda ya bayyana gamsuwa kan kudirin gwamna Muhammad Badaru Abubakar na sake gina hanyar Gwaram zuwa Basirka, ya ce hanyar wace ta hade jihohi da dama zata kara habaka tattalin arziki dana sufuri a tsakanin jigawa da sauran jihohi.
Dan majalisar wakilan ya ce kasancewar ya gabatar da kudirin sake gina hanyar a zauren majalisar wakilai ta kasa, ya ce koda gwamnan ya gudanar da aikin sake gina hanyar lashakkah gwamnatin tarayya zata biya shi kudin aikinsa daga baya.
Alhaji Yuguda Hassan Kila ya kara da cewa akwai ayyuka da dama da wannan gwamnati ta bujiro da su domin ingata rayuwar al’umma a kowane mataki, sai dai kuma ya bukaci al’umma su ci gaba da hakuri da kuma marawa gwamnati baya.
Daga Profile din Hussaini Hadejia.