The Northern Nigerian Governors/Islamic Development Bank (IDB) meeting witnessed the third and last day in Jeddah, Kingdom of Saudi-Arabia.
The round-off meeting was chaired by the Vice President Operations of the Bank Dr. Mansur Mukhtar in a closed door with the Governors and some top officials managing the Bank subsidiaries, after which a technical committee was set up to look at the Nigerian laws, business advantages of the Region, and design plans towards the agreements reached with the Governors, and prioritize on the sectors that need immediate considerations.
However, the Jigawa State Governor Alhaji Mohammad Badaru Talamiz (MON, mni) have proceeded to the Holy City of Madina to pay homage to the Holy Prophet Muhammad (SAW), from there he will be proceeding to the Holy City of Makkah to perform a Lesser Hajj (UMRAH), and pray to Almighty Allah to grant him the will and wisdom to deliver the stewerdship entrusted on him.
The Governor is expected back home on Saturday.
***********************************
A yau Taron Gwamnonin Arewacin Najeriya da Jami'an Bankin Cigaba na Musulunci ya cika kwanaki uku wanda kuma shine ranar karshe na zaman, a Birnin Jeddah dake Kasar Saudi Arabia.
Wanda ya jagoranci taron karshen shine Mataimakin Shugaban Bankin Data Mansur Mukhtar a wani zama da yayi na sirri tsakanin Gwamnonin da wasu manyan jami'an Bankin.
Bayan taron an kafa wani kwamiti da zai yi duba na tsanaki akan dokokin Najeriya, da kuma yanayin kasuwancin yankin Arewacin Najeriya, da nufin yin wani tsari domin cimma burukan abinda aka tattauna tsakanin hukumomin Bankin da gwamnonin domin duba bangarorin da suka fi muhimmanci da za a fara maida hankali a kansu.
Bayan Kammala taron ne, Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) ya wuce garin Madinah domin ziyara ga Manzo Annabi Mohammad (SAW), inda bayan ziyarar zai wuce Makkah domin aikin Umrah, da kuma rokon Allah (SWT) ya bashi ikon sauke nauyin dake kansa na al'umar Jihar Jigawa.
Ana sa ran Maigirma Gwamnan zai dawo gida Najeriya a ranar Asabar mai zuwa Insha Allah.
Da fatan Allah ya dawo mana Hadimin Al'umar Jihar Jigawa lafiya, ya karbi ibadah (amin).
Auwal D. Sankara,
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
02/02/2016
Abdullahi Umar Chamo
- Solvetor -
State Vice Chairman
Tsinkaya Social Network
No comments:
Post a Comment