Jigawa State Government has attributed the delay in the last month salary as a result of the change of Monthly Federation Account Meeting.
The Acting Governor, Barrister Ibrahim Hassan Hadejia stated this while briefing newsmen in his office.
Barrister Ibrahim Hassan was commenting on rumors being speculated on the delay on payment of last month salary by the State Government.
The Acting Governor who described the economic meltdown as the main challenge facing governments at all levels said presently about Thirteen Local Governments could not pay Workers Salary without State Government bail out.
He said a number of policies and majors have been taken to ensure smooth running of government activities due to the financial crisis in the country.
Speaking on improving the internally generated revenue (IGR), Barrister Ibrahim Hassan explained that government is looking at the possibility of updating
Laws governing revenue collection in the State.
He also called on the people to understand the present situation and support government in its effort to revamp the state ailing economy.
**********************************
Gwamnatin Jihar Jigawa ta alakanta tsaiko da aka samu na biyan albashin watan da ya gabata saboda canjin da aka samu wajen gudanar da taron Kasafta Kudi daga asusun tarayya.
Mukaddashin Gwamnan Jihar Jigawa Barista Ibrahim Hassan Hadejia, shi ya bayyana haka a sanda yake zantawa da manema labarai a Ofishinsa.
Mukaddashin Gwamnan yayi wannan tsokaci ne saboda irin jita-jita da ake ta adawa saboda rashin biyan albashin da ba a yi akan lokaci a Jihar ba.
Mukaddashin Gwamnan, wanda yace karyewar tattalin arziki shine babban kalubale da Gwamnati a kowane mataki ke fuskanta, yace a halin yanzu kusan Kananan Hukumomi goma sha uku basa iya biyan albashin ba tare da dafawar Gwamnatin Jihar.
Yace Gwamnatin ta fidda wasu tsare-tsare tare da daukan wasu matakai domin samun saukin tafiyar da ayyukan Gwamnatin saboda karancin kudi da Jihar keep fama dashi.
A yayinda yake magana akan baton inganta hanyar samar da kudaden shiga na cikin gida, Mukaddashin Gwamnan yace Gwamnatin Jihar tana nazari domin ganin ta karfafa dokar karbar haraji a Jihar.
Anan ne yayi kira ga jama'a da su fahimci halin da ake ciki, su dafawa Gwamnati a kokarin da take yi na farfado da tattalin arzikin Jihar da ciyar da ita gaba.
Auwal D. Sankara,
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
04/02/2016
Abdullahi Umar Chamo
- Solvetor -
State Vice Chairman
Tsinkaya Social Network
08067323407