Adsent

Monday, 16 November 2015

GWAMNA YA KAI ZIYARAR TA'AZIYYAR NASIRU HABU BABURA.

Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) yace rashin Nasiru Habu Babura babban rashi ne ba wai ga Iyalansa kadai, rashi ne ga daukacin al'umar Jihar Jigawa,musamman yan jam'iyyar APC.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin da ya ziyarci gidan iyalan Marigayin a garin Babura domin yi musu ta'aziyar wannan rashin.
Marigayin wanda Allah ya masa rasuwa ranar Juma'a da ta gabata shine Shugaban Kungiyar APC Social Media na Jihar Jigawa.

Labarin rasuwar ya riski Maigirma Gwamna ne a yayinda yake wajen taron bita a Kaduna inda tun a can ya bayyana alhininsa da wannan babban rashi ga Iyalan mamacin, al'umar Karamar Hukumar Babura da Jihar Jigawa.

Gwamnan yace halayen mamacin kyawawa ne abun koyi kuma ya bayar da gudunmawa mai yawa musamman a lokacin zabensa na
Gwamnan Jihar Jigawa musamman a shafukan sada Zumunta. Kamar yadda Gwamnan yace "Rayuwar Nasiru Habu ya taba mutane da yawa, kuma yana da masoya da yawa, shi yasa rasuwar sa ya taba
mutane da dama a garin Babura da Jihar Jigawa musamman a shafukan sada Zumunta".Gwamnan yayi addu'ar Allah ya jikan mamacin,
ya kuma yi masa sakayya da gidan Aljanna. Gwamnan yayi amfani da damar domin yin wasu ta'aziyar a garin na Babura inda ya fara da
gidan tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Jigawa Alhaji Adamu Dan Gile Babura wanda ya rasa mahaifiyar sa.
Sannan ya kai wasu ta'aziya a gidan Malam Abdullahi Gumal Babura da gidan Malam Danazimi Odar Babura da kuma gidan Hajiya Ma'u Yakubu Babura.

Auwal D. Sankara, Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State On New Media.

posted from Bloggeroid

Tuesday, 10 November 2015

TATTAUNA KASAFIN KUDI NA SHEKARAR 2016........

TSINKAYA SOCIAL NETWORK

TATTAUNA KASAFIN KUDI NA SHEKARAR 2016........

Domin cimma nasarar tsare-tsaren gwamnatinsa da cika alkawuran da gwamnan yayi a lokacin Yakin neman zabe, Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa ya fara zaman tattaunawa da jami'an gwamnati (kwamishinoni) da Ma'aikatan

gwamnatin akan kasafin kudi na kowacce Ma'aikata wanda shine zai zama kasafin kudi na shekara 2016, kuma na farko a wannan gwamnatin ta Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa

Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON,mni) .

Taron tattaunawar ya hada da kwamishinoni da Manyan Sakatarori na ma'aikatun Jihar Jigawa. Taron tattaunawar an fara shi a jiya Litinin tare da Ma'aikatar Yada Labarai,matasa, Wasanni da Al'adu.

Auwal D. Sankara, Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State On New Media (Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa A Sabbin Kafafen Sadarwa) 10/11/2015.
TSINKAYA SOCIAL NETWORK

4rm. Saifullahi Abbas Hadejia AUDITOR GENERAL TSINKAYA SOCIAL NETWORK

posted from Bloggeroid

TATTAUNA KASAFIN KUDI NA SHEKARAR 2016........

SECTORAL BUDGET DELIBERATIONS AND DISCUSSIONS FOR 2016 ANNUAL BUDGET..........
To achieve or implement the policies and programmes of his administration to reflect the promises and pledges made during the campaign the Executive Governor of Jigawa State has started having asectoral budgetdiscussions which will be deliberated by the various Ministries, Departments and Agencies (MDAs) along with the Executive Governor ahead of the 2016 Budget which will be the first that will be presented by His Excellency Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) as an
Executive Governor of Jigawa State.

The Discussion Parley includes the Honourable Commissioners and Permanent Secretaries of their respective Ministries.

The Sectoral Budget Discussions started yesterday with the Jigawa State Ministry of Information,Youths Sports and Culture.

**