1- Gwamnan jahar Ebonyi David Umahi ya yiwa wani sakataren dindindin (Permanent Secretary) jahar ritayar dole,Bayan da ya kasa lissafa adadin kudaden ma'aikatan da suka kammala aiki (Gratuity)
2- Kungiyar ' Yan tawayen dake rajin kafa kasar Biafra ta IPOB tace ZUNUFIN da Shugaba Buhari ya dauka akansu bazasu ta6a yafe Masa ba
3- Alh Atiku Abubakar ya yi ikirarin cewar yafi Cif Ahmed Bola Tinubu cancantar zama Shugaban Nageriya domin ba a Ta6a zarginsa da Ta'ammuli da Miyagun Kwayoyi ba
4- Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kaduna ta bawa iyalan tsohon Shugaban Kasar Nageriya Sani Abacha Nasara akan karar da suka shigar na Rushe Otel dinsu Mai suna ( Durbar Hotel) da Gwamnan jahar Malam Nasiru Elrufa'i yayi a Shekara ta 2020
5- Tsohon Gwamnan jahar Kano Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce zai zama mashawarci ga Za6a66an Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf kuma yace za' tabbatar an gyara duk wata 6arnar da akayi da kuma kwato hakkin Al'ummar jahar
6- Gwamnatin tarayya tace duk Shekara mutane kusan Miliyan 55 suke kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro ( Malaria) kuma mutane dubu 90 ne ake bada ruhoton mutuwarsu sakamakon cutar
7- Shahararran Masoyin Nan na Shugaba Buhari kafin daga bisani ya zama makiyinsa wato Dan Bilki Kwamonda ya yi kaukausan suka akan Ministan sadarwar kasar Isa Ali Pantami inda ya ce Malamin baya Abu don Allah kuma Malami ne Dan FASHION
8- Kungiyar Masu gidajen Buredi ta( Bakers) tace sama da gidajen Buredi Dubu 26 aka rufe cikin Shekara 8 da Shugaba Buhari yayi yana Mulki
9- A wata takarda da Dakaceccen kwamonshinan zabe na jahar Adamawa Hudu Ari Yunusa ya akewa Rundunar'yan sanda da kuma ta farin Kaya SSS ya fadi sunayen wasu kwamanshinonin zabe 2 wato Abdullahi zuru da Baba Bila da cewar su suka taimaka Masa da Alkaluman boge domin ayi Magudi.
Menene Ra'ayin ka ki ko wani labari yafi Jan hankali?
Daga Usman Rangis.