TSINKAYA SOCIAL NETWORK...
A yau Talata 31/07/2018, maigirma mataimakin gwamnan jihar Jigawa Barrister Ibrahim Hassan Hadejia ,(Shettiman Hadejia na II) ya kai ziyara katafaren Kamfanin Sugar dake Karamar hukumar Gagarawa. Wannan kamfani tuni ake gudanar aiki ba tare da bata lokaci ba, in dai ba'a manta ba kwanaki Gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da aikin wannan kamfani a garin na Gagarawa.
Maigirma mataimakin gwamnan ya samu tarba daga babban jami'in gudanar da wannan aiki, inda ya zagaya dashi sassan kamfanin domin ganewa idonsa yadda aikin ke tafiya. Tareda kai ziyara zuwa daya daga cikin gonakin Rake, domin ganewa idonsa yadda ake gudanar da noman Raken.
Shettiman na Hadejia ya yaba da yadda yaga aikin ke tafiya, tare da kira ga ma'aikata su sake zage damtse wajen gudanar da aikin domin samar da wuraren aikin yi ga matasa wannan jiha dama sauran jihohi makwafta.
Kamfanin dai zai samar da guraben ayyukan yi ga dubban matasa dake wadannan yankuna dama sauran yankuna na wannan jiha.
Photo: Ahmad Haruna (Direktan yan jaridu na ofishin mataimakin gwamnan jihar Jigawa).