MA'AIKATAR SHARI'A DAKE JIHAR JIGAWA
Wata Kotu a Jihar Jigawa Karkashin Jagorancin Kwamishinan Shari'a na jihar Barr. Sani Husssini G/Gabas ta yanke hukuncin kisa ta hanyar Rataya ga wani matashi...
Kotun Shari'a Dake Birnin Kudu High Court 2 Ta Yankewa Adamu Audu Dan Shekara 35 Mazaunin Kauyen Tudun Malam Dake Karamar Hukumar Birnin Kudu Jihar Jigawa, Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya!
A Ranar 1-4-2015 Da Misalin Karfe 12 Na Rana, Wani Mutum Mai Suna Adamu Audu Wanda Ake Tuhumar Sa Da Kisan Kai Ta Hanyar Cakawa Wani Matashi Wuka A Ciki, Mai Suna Garba Khalid Dan Shekara 30, Mazaunin Kauyen Tudun Malam Dake Karamar Hukumar Birnin Kudu, Cikin Jihar Jigawa.
Bayan Kotu Ta Tabbatar Da Laifin Kisan Kai A Kansa Wajen Samun Gamsassun Shaidu, Da Kuma Ikrari Da Yayi Da Bakinsa, Alkalin Kotun Hon. Judge. Ahmed Mohammed Kazaure. Wanda A Jawabin Makashin Yace, Yana Zargin Marigayinne Da Maita, Hakan Yasa Ya Kashe Shi. Wanda Kotu Tace Masa Wannan Bazai Zama Hujja A Gareshi Ba
Kotu Ta Yanke Masa Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya Karkashin Kashi Na 221 Kundin Laifuffuka Na Jihar Jigawa (Jigawa State Fenal Code Section 221)
Allah ka tsaremu da biye wa zuciya.
-Saifullahi Abbas Hadejia
New Media Correspondent
Ministry Of Justice
Jigawa State, Nigeria