
Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar (MON, mni) yana jajantawa ɗaukacin al'umar Jihar Jigawa musamman al'ummomin Ƙananan Hukumomi da yankunan da ambaliyar ruwa ya masa ta'adi.
Haƙiƙa wannan ibtila'i yana zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnatin Jiha ta tashi haiƙan wajen ganin an kawo ƙarshen ire-iren waɗannan matsaloli na din-din-din, duba da irin hoɓɓasa da gwamnatin ke yi na samar da tituna da magudanan ruwa a duk faɗin Ƙananan Hukumomin Jihar.
Duk da cewa Hukumar dake Harsashen Yanayi tace za'a samu Ambaliyar Ruwa a wasu Jihohi har da Jigawa, sannan Hukumar bada agajin gaggawa ta gargadi al'ummomin jihohin da ma wadanda suke makwaftaka dasu da suyi taka tsantsan, hakan ne yasa gwamnati ta tashi haiƙan don ganin an rage ƙarfin wannan matsaloli a gajeren zango da kawo ƙarshensu gaba ɗaya a dogon zango.
Maigirma Gwamna ya bada umurni a kafa Kwamiti mai Ƙarfi da zai zagaya ya duba irin ɓarnar da ruwa yayi da nufin kawowa waɗanda abun ya shafa agaji na gaggawa.
Maigirma Gwamnan yayi kira ga jama'a da su ƙara kula sosai wajen ganin an kare afkuwar hakan ta hanyar gyaran magudanan ruwa da yin cikon ƙasa a wuraren da ake buƙata, kuma ita ma a nata ɓangaren gwamnati zata shigo gadan-gadan don magance matsalar gaba ɗaya.
A ƙarshe Maigirma Gwamnan yayi addu'ar Allah ya kare afkuwar hakan nan gaba, ya kuma maida alherin abinda aka rasa.
Auwal D. Sankara,
Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa.
12/08/2016
posted from Bloggeroid