The Executive Secretary, Jigawa State Agency for Nomadic Education, Alhaji Ali Manu says that the State Government had concluded plans to establish 14 additional nomadic schools in the state.
Manu told Jigawa State New Media Office that the schools would be established in Kwangara village in Birninkudu, Kafin Baci in Kiyawa, Kulma in Jahun, Ardo Usaini in Gumel, and Kutum in Malammadori.
He said that others would be established in Kubayi in Guri, Modibawa in Miga, Jawura in Buji, Muwi in Babura, Gallekyar in Giwa and Wangara and Dojar in Dutse.
The Executive Secretary said that the State Government had also planned to renovate the existing 10 nomadic schools in some selected local government areas of the state.
He said those to be renovated were in Ladduga in Birnin Kudu, Kufito in Kaugama, Ketawa in Maigatari, Gezojin Wambai in Kazaure, Barnawa in Taura and Dolel Dabdili in Kirikasamma.
According to him, the building of new schools and renovation of existing ones are meant to increase enrolment of children in nomadic schools in the state.
Manu said that the measures would also enhance attendance among the children of nomads as well as boost the level of literacy at the grassroots.
He said that the agency had over time, in collaboration with Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MCBAN) in the state, senstised nomads on the importance of education.
The Executive Secretary urged the would-be beneficiaries to complement the government's effort by enrolling their children in the schools.
Manu also urged them to use the opportunity to encourage their children and wards to be educated to enhance their future prospects.
*************************************************************************
Babban Sakataren Hukumar Ilimin Makiyaya na Jihar Jigawa Alhaji Ali Manu yace Gwamnatin Jiha ta kammala shirye-shiryen ta na samar da karin Makarantu sha hudu na Ilimin Makiyaya a Jihar.
Manu ya gayawa Ofishin Sabbin Kafafen Sadarwa na Jiha cewa za a samar da wadannan makarantun ne a kauyen Kwangara dake Karamar Hukumar Birninkudu, Kafin Baci a Kiyawa, Kulma a Jahun, Ardo Usaini a Gumel, da Kutum a Karamar Hukumar Malammadori.
Yace sauran za a samar dasu ne Kubayi dake Karamar Hukumar Guri, Modibawa a Miga, Jawura a Buji, Muwi a Babura, Gallekyar a Gwiwa, sai Wangara da Dojar a Karamar Hukumar Dutse.
Babban Sakataren yace haka kuma gwamnatin Jihar ta shirya gyara makarantun Makiyayan guda goma da ake dasu a wasu kananan hukumomi, inda yace makarantun da za a gyara sun hada da wadanda suke Ladduga a Birnin Kudu, Kufito a Kaugama, Ketawa a Maigatari, Gezojin Wambai a Kazaure, Barnawa a Taura da Dolel Dabdili dake Karamar Hukumar Kirikasamma.
A cewarsa, za a gina sabbin da gyara wadanda ake dasu a Kasa ne da nufin kara fadada Ilimin makiyayan da kara samun wadanda zasu shiga makarantun domin neman Ilimi.
Manu yace wannan matakin zai kara yawan masu shiga makarantun tare da kara yawan wadanda suka iya karatu da rubutu musamman a rugage.
Yace Hukumar tasa a halin yanzu ta hada gwiwa da Kungiyar Makiyaya na Miyetti Allah na Jihar Jigawa domin wayarwa da makiyayan kai akan muhimmancin neman Ilimi.
Don haka ne Babban Sakataren Hukumar yayi kira ga wadanda zasu ci moriyar shirin da su bawa gwamnatin hadin kai wajen sanya 'ya'yansu a makarantun.
Karshe Alhaji Manu yayi kira ga iyayen yara makiyaya da su karfafa wa 'ya'yansu gwiwa wajen neman Ilimi domin rayuwarsu ta inganta nan gaba.
Auwal D. Sankara,
Special Assistant to the Executive Governor of Jigawa State on New Media
(Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa)
28/01/2016.